Disneyland 1972 Love the old s

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah SHIN CEWA YAYI SIYASA TAFI SALLAH A 'DAN WANI TSURKUKIN YANAYI KO KUMA CEWA NE
YAYI ''SIYASA TAFI SALLAH MUHIMMANCI A KULLU YAUMIN''? (SOURCE: AL-ANSAR ISLAMIC
FOUNDATION ZARIA VIA FATAWA ASH-SHEIKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI VOLUME 2 WALLAFAR MUSA LAWAL FUNTUA.)
.
ALLAHU AKBAR! TSARKI YA TABBATA GA ALLAH. WANI GOMA DA GOMA SAI 'DANGATA.
.
GA BAYANIN GASKIYA DAGA BAKIN BABBAN MALAMI, MAI KUJERA A MAJALISAR MALAMAN DUNIYAR ZAMANINSHI, ALKALIN AL'KALAN
AREWACIN NIGERIA, DA'YA TAMKAR DA DUBU INJI ASH-SHEIKH AUWAL ADAM ALBANI ZARIA, MAI ILIMI DA HANGEN NESA ASH-SHEIKH ALKALI ABUBAKAR MAHMUD GUMI.
.
TAMBAYA: Akramakallahu! A karatun ba'ra, kaace: 'siyasa ta fi sallah muhimmanci.'To muna son sanin in da ka dogara?
.
AMSA:To, wannan bayani haka abin ya ke. Wato, cewar da na ke yi ''siyasa tafi muhimmanci bi sa ga sallah, haka ne. Domin da siyasar ake yin shugabanci, kuma da shugabancin nan za'a gudanar da makarantu, da kotuna, da tsaro, da masallatai, da dai duk al'amuran kasa. Shine Allah (S.W.T) ke cewa: ALLAZINA, IM-MAK
KANNAHUM-FIL-ARDI,AKAMUS-SALATA. Wato, ''wadanda ya ke idan muka ba su iko a cikin kasa, za su tsaida sallah, su ba da zakkah, su yi umurni da abin da aka sani.'' (suratul Hajji, aya ta 41).
.
To shine akace shugabanci na tsare abubuwa shidda. Wadanda sune ita kanta ibadar gaba dayanta, shugabanci ne ke
tsare ta, don ayi ta da kyau.
.
Sannan shugabanci na tsarewar Nasarar mutane, da dukiyar mutane, da rayukan mutane, da
hankulan mutane, da kuma mutuncin su.
.
Duk wadannan sune shugabancin Musulunci ke tsarewa. To, da kuma siyasar ake yin shugabancin. To, daidai ne duk abar wadannan abubuwa a hannun wadanda ba
Musulmi ba?
.
Bayan hakanan, ku duba! A kowane gari da kuka sani, sarkin garin nan, ko Hakimin garin nan, ko dagacin garin nan yafi limamin
garin daraja ga idanun mutane, don haka barnar da sarkin nan zai iya hanawa liman bai iya hanawa. Domin yawancin ma sarakunan ne ke na'dawa ko cire limaman.To, ashe kenan shugabancin ne a
gaba. To, yana yiwuwa kace to ai duk wannan siyasar da shugabanci da ake gudanarwa ba na musulunci ba ne, balle ace har sun fi sallar muhimmanci. To, kuna son su cigaba da gudana ba irin na musuluncin ba? Idan kuna son su koma irin na musuluncin ya ya za'ayi? Dole sai kun shige su, kuna gyarawa a hankali-a hankali har ku gyara baki daya, gwagrwadon ikon ku.
.
Hakanan, kun ga nifa idan mutum bai yi sallah ba, laifin rashin yin sallar nan shi kadai abin ya shafa ko iyalan shi ma bai shafa ba
domin 'FARRUL-AININ' ce, wato abin shi kadai ya shafa. Amma in bai yi siyasa mai kyau ba ta Musulunci ba, abin ya shafi kasar
sa duka ma'ana ya shafi iyalansa, ya shafi garinsu, ya shafi dai duk kasar sa duka.
.
Don haka, idan yace tun da dai ba da musuluncin ake gudanar da su ba saboda haka ya bar abin a hannun kafurai kawai toh ya ja abinda zai kai kasar ga kafurai da
kuma cigaba da kafurcin. Anan idan rashin yin sallar sa ta tsaya ga zunubin shi shi kadai, to mugunyar siyasa zata kai ga
kafurcin kasa gaba daya. Saboda haka babu wani rikici ga wannan. Domin da siyasar nan ana iya kawo yadda za'a gyara
abubuwan addinin mu gaba daya. Idan kuma muka kyale ana iya kawo abinda zai cutar da addinin mu gaba daya. Misali shine;
da siyasar nan ana iya kawo tsarin da za'a gyara makarantu mu su zan irin tsarin Musulunci, haka ana iya kawo tsarin da za'a gyara kotunan mu su zan irin tsarin shari'ar Musulunci. Dominku duba yadda tsarin kotunan mu suke a halin yanzu; yadda za'a zalunci mutum, wato ya kai kara domin a bi masa hakkin shi amma sai ayi ta wahalar dashi har ya gwammace bai kai karar ba, toh idan ana shari'ar musulunci, duk
wannan na faruwa? To, da yaya za'a gyara shari'un kotunan har su komo ga shari'ar musulunci, ta yadda wanda ma ba musulmi
ba zai bukaci a kai shi kotun Musulunci idan ba mun yi siyasar ba har mun zabi mutanen kirkin da zasu gyara mana wadannan
abubuwa ko da kuwa a hankali a hankali ne.
.
Saboda haka, har yanzu dai babu wani rikici ga wannan bayani da na ke yi.
.
ALLAH KA GANAR DA WANDA BAI GANE BA, KU NEMI GASKIYA YAN BIDI'A SAI ALLAH YA TAIMAKE KU ''WALLAZINA JAHADU FIHA...........
.......''
2018-06-26 05:48 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 7 user
This Week : 30 user
This Month : 17 user
Total all : 270283 visitorsUnited States
LAST PAGES