Pair of Vintage Old School Fru

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah SHIN MAI CIKI TANA YIN HAILA ? Tambaya:
Malam mai ciki za ta iya ganin Haila? Amsa: Yawanci idan mace ta dau ciki jini yakan daina zuwa mata, Imamu Ahmad yana cewa (Mata suna gane samuwar ciki da yankewar jini) Idan mace mai ciki ta ga jini idan hakan ya kasance kafin haihuwa da kwana biyu ko uku kuma a tare da shi akwai ciwon haihuwa to wannan jinin haihuwa ne, idan kuma kafin haka ne da lokaci mai tsawo, ko kuma tsakaninsa da haihuwa ba yawa amma ba zafin haihuwa to wannan ba biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen haila ba za su shafe shi ba? Anan malamai sun yi sabani: Abin da yake daidai shi ne jinin haila ne in dai ya zo a yadda ta saba yin jinin haila, saboda asali duk jinin da ya zowa mace ana daukarsa a jinin haila, in dai ba akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba, kuma babu wani dalili a alqur’ani ko a sunna da zai hana shi ya zama haila. Wannan shi ne mazahabar Maliku da Shafi'i, kuma Baihaki ya hakaito hakan daga cikin maganganun Ahmad. Don haka yana tabbata ga mai ciki mai haila abin da yake tabbata ga mai haila mara ciki sai a gurare guda biyu : 1. SAKI- Ya haramta a saki matar da idda ta wajaba a gare ta idan tana haila, amma mai ciki ya halatta a sake ta a cikin haila, saboda sakin matar da bata da ciki ya sabawa fadin Allah ( Kuma ku sake su a farkon iddarsu) Suratud Dalak aya ta 1, wato a farkon tsarkin da bai take ta a cikinsa ba. amma sakin mace mai ciki tana haila sakin ta ne ga iddarta, wannan ya hada da tana cikin haila ko tana cikin tsarki, saboda iddarta tana kasancewa ne da haife wannan ciki, don haka bai haramta a sake ta ba, bayan an yi jima’i da ita. 2. mace mai ciki idan ta yi haila ba za ta yi idda da ita ba, saboda iddar ta tana kasancewa ne da haife cikinta, wannan ya hada da tana haila ko bata yi, saboda fadin Allah madaukaki ( Iddar mata masu ciki tana kasancewa ne idan su ka haife cikinsu). Suratud Dalak aya ta 4 Don neman karin bayani duba : Dima'uddabi'iyya shafi na 11.
Jamilu Yusuf Zarewa
2018-02-05 08:44 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 43 user
This Week : 43 user
This Month : 996 user
Total all : 271262 visitors
LAST PAGES