Polly po-cket

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah SHIN YA HALASTA IN FARA SITTU SHAWWAL KAFIN RAMUWAR RAMADAN???*
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakaatuhu,
Lallai wannan tambaya ce da ta yawaita a tsakanin al’ummar Musulmi, musamman Mata, don haka ya sanya zan yi rubutu in fadi matsayar Malaman SUNNAH akan haka, gwargwadon abin da Allah Ta’ala Ya hore mun:
1. An tambayi Sheikh Abdulaziz Bn Baz, Allah Ta’ala Ya yi masa rahama, cewa:
Shin ya halasta in azumci sittu Shawwal, alhalin a na bi na azumin watan Ramadan?,…
Sai ya amsa da cewa: “Abin da yake wajibi shi ne Mutum ya fara ramuwa kafin sittu Shawwal, ba zaka azumci sittu Shawwal ba har sai ka kammala Ramadan, domin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, cewa ya yi:
” Duk wanda ya azumci watan Ramadan, sannan ya biye masa da shida daga cikin watan Shawwal… ”
Don haka duk wanda akwai ramuwa a kansa har yanzu bai kammala Ramadan ba, akwai saura a kansa, kuma sittu Shawwal ana yin sa ne bayan kammala Ramadan. Don haka wajibi ne Mutum ya fara da ramuwa kafin sittu Shawwal.
Wannan fatawa Malam Bn Baz, Allah Ta’ala Ya yi masa rahama, ya yi ta ne a
Nurun ala Darb wanda sunan wani shiri ne da yake gabatarwa a Iza’atu Qur’anul Kareem a kaset na 918.
2. An tambayi Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani, Allah Ta’ala Ya yi masa rahama, cewa:
Shin sharadi ne ga wanda yake so ya yi azumin sittu Shawwal dole sai ya kammala ramuwan Ramadan?
Sai ya amsa da cewa:
“Na’am, saboda domin wajibi ake gabatarwa akan nafila, kuma dan Adam ba ya mallakan kansa da rayuwarsa domin mutuwa za ta iya zuwa masa a kowane lokaci…
Malam Albani, Allah Ta’ala Ya yi masa rahama, ya amsa wannan tambaya ne a silsitul Huda wannur, wato jerin kaset-kaset da suka tara fatawoyinsa, a kaset na 753.
3. An tambayi Sheikh Muhammad Saleh Al-Uthaimeen, Allah Ta’ala Ya yi masa rahama, cewa:
Inda a ce Mutum zai azumci sittu Shawwal kafin ya yi ramuwar azumin Ramadan, shin wannan azumin zai amfane shi? Kuma wannan ya wadatar ba sai ya sake sittu Shawwal ba?
Sai ya amsa ya na mai cewa:
A’a, ba zai amfane shi ba, domin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya na cewa: “Dukkan wanda ya azumci watan Ramadan, sannan ya biye masa da shida daga cikin Shawwal”. Kuma sanannen abu ne dukkan wanda ake bin sa ramuwa har yanzu bai kammala Ramadan ba…
Don haka, inda Mutum zai fara da sittu Shawwal kafin ramuwar Ramadan, ba zai samu ladan da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ambata ba, domin cewa ya yi: ” Duk wanda ya azumci watan Ramadan, sannan ya biye masa da shida daga cikin Shawwal…” Muslim ya ruwaito hadisin.
Yan uwa wannan a takaice kenan, abun lura shi ne LALLAI BA A FARA SITTU SHAWWAL KAFIN RAMUWA, musamman yanda Malam Albani, Allah Ya yi masa rahama, ya ce rayuwa bata da tabbas mutuwa na iya riskan Mutum a Koda yaushe, kuma farillai za a fara bincikan mu kafin nafilfili, kuma babu inda a shari’ar Musulunci ake gabatar da nafila akan farali.
Allah Ta’ala Ya taimake mu, in sha Allahu Ta’ala gaba kadan zamu ji, SHIN YA HALASTA GA WANDA YA KARAR DA WATAN SHAWWAL WAJEN RAMUWAN RAMADAN, DA YA YI SITTU SHAWWAL DIN SHI A WATAN DA KE GABAN SHAWWAL???, sannan kuma zamu ji shin akwai wata falala da fifiko ga wanda ya jeranta sittu Shawwal akan wanda bai jeranta ba???.
Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria._*
20/07/2015.
Wanda ya yi bitan wannan rubutu:
Malamina Dr Ibrahim Disina.
Allah Ta’ala Ya saka masa da alheri
2018-06-17 20:06 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 9 user
This Week : 32 user
This Month : 19 user
Total all : 270285 visitorsUnited States
LAST PAGES