Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah SHIN YA HALATTA MATAR AURE TA YI FACE BOOK ?
Tambaya : Assalamu alaikum, shin ko ya halatta ga matar Aure ta yi face book, harma da charting ? Amsa : Wa alaikum assalam Wannan tambaya ce mai wahala. Saidai abin da zance duk abin da zai amfane ta za ta iya yi a face book, saboda asali a shari'ar musulunci, duk abin da mutane suke aikatawa a mu'amalarsu ta yau da kullum halal ne, mutukar ba'a samu wani nassi wanda ya haramta ba, ko kuma ya kasance cuta tsantsa, haka ma idan mafi rinjayansa barna ne, ka ga face book kuwa babu wani nassi da ya haramta shi, sannan ba cuta ba ne tsantsa, tun da ana iya samun ilimin addini ta wannan kafa. Ya kamata ta daina yin charting da wadanda da muharramanta ba in ba malamin da ta yadda da iliminsa da tsantseninsa ba, za ta yi masa fatawa, saboda akwai maza da yawa da suke bi ta hanyar charting don lalata matan auren da ba su da kamewa. Wannan ya sa barin charting da mazan da ba muharramai ba, ko kuma wadanda suke neman auran matar, zai iya zama wajibi, saboda hakan yana kaiwa zuwa barna, duk abin da yake kaiwa zuwa barna, zai iya zama haramun ko makaruhi, kamar yadda malaman musulunci suka tabbatar. Allah ne mafi sani.
Dr. Jameel Zarewa.
2018-01-21 15:43 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 4 user
This Week : 560 user
This Month : 802 user
Total all : 271068 visitorsUnited States
LAST PAGES

Teya Salat