Pair of Vintage Old School Fru

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah JAGORORIN SHIRI:
.
→Shamseeyah Alhassan Muh’d
.
→Faridah Bintu Salis (Bintus-sunnah)
.
Wanda Yazo kamar haka: Ranan Talata 26/12/2017 Insha ALLAH.
.
LOKACI: 8:00pm zuwa 9:30:pm Na Dare.
.
Kad’an daga cikin abunda Matan ZAUREN MUSLIM UMMAH suka ce dangane da Topic din: ↓↓↓
.
______________________________
→Imranat Ado Bello tace: A,uzubillahis sami,I’ll alim minashshaidanir rajim bismillahirrah manirrahim wassalatu wassalamu ala rasulullah, Assalamu Alaikum warahmatullah, yan uwa masu girma tunda anbuqaci members su tofa albarkacin bakinsu, ina ga yawancin masu aikata hakan nafarko akwai tsantsar jahilci agare su sannan dakuma son zuciya da zargi
.
Aure sai anyi haquri sannan ki koya mata dabarun zama da miji da yan uwansa, amma baza ,ayi hakaba saidai dasabani yahadasu zakaji anacewa mijin wance bashi da mutumci da sauransu ace ke inya matsa miki taho kibar masa gidan sannan bangarena biya ace dankine ya auro yar wayansu to wannan yafi tashin hankali awurin wasu.
.
______________________________
→ Aisha Idris tace: Assalama alaikum ni Ina ganin qarancin ilimin addini Na da tasiri a rayuwar yanzu. Sannan da daukar kalmar wayewa Wanda ke haifar da rashin kunya tunda a baya iyaye basa shiga tsakanina yayansu da surukai in ba matsala CE ta tasoba.
.
______________________________
→Aisha Imam tace: Assalamu alaikum Yan uwana masu albarka hakan yana faruwa sosai acikin Al,umma amma jahilci shine jagora darashin sanin girman kai darashin sanin mutuncin kai.
.
Da zubar dakima da zubewar mutunci
.
In iyaye sunsan mutuncin Kansu bakomai bane zasu dinga shiga sha,anin rayuwan auran yayansu.
.
Nagartacciyar uwa ko qarar maigidanka ka kai zata ce kaje kayi haquri domin nima haquri nake yi har kuka kai munzalin yanzu ko bakyaso ki rayu da yaranki watarana ace kin aurar su, don haka maza ki koma d’akinki kiyi haquri kada ma ki bari mahaifinki yazo ya same ki anan.
.
Allah yasa mudace.
.
_____________________________
→ Nusaiba Adam tace: Da farko dai abunda ke jawo hakan akwai son xuciya da son abun duniya.
.
______________________________
→Ummu Safiyya tace: Assalamu Alaikum
.
Hakan na faruwa kam Yawanci abinda ke jawo hakan farko sai kiga yarinya duk abinda ya faru tazo ta gaya ma uwa
.
Bakowa ni abune za’a gayama iyayeba saikiga abinda ba sai iyaye sunji ba yarinya zata kwashi jiki taje tagaya ma uwa
in akai rashin sa’a uwar gata ga kamanta ne tanan zata riqi Mijin, ita kuwa ‘yar kiga sunshirya da Mijin uwar nanan riqe da abin, Bai kamata ko wani matsala a gaya ma iyayeba inba dai babbar matsalaba Wanda ba’a fata.
.
_____________________________
→Hindatu Junaid tace: Agsky mafi yawan iyaye mata sunasa kwaladayi ciki alamuran aure yayansu duk lkc diyarsu tayi aure sundiga tambayar wane hali take ciki yaya zamansu yake tahaka har sukai da jin abunda baimusu dadiba daganan sai anyi ance yashiga koda diyar batadamu har abun yazo yafara damunta sai tafara bijire ma mijinta daga itako uwa mace tasamu abunda take sai ta shi ga har azoga mutuwar aure har inmijin talakane ngd.
.
______________________________
→ Ummu Aliyu Zaria tace: Mafiyawan mutane basa daukan aure amatsayin ibadah, sunfi dakwanshi amatsayi najin dadi da holewa. Shi ibada kuwa abune nadole da hakuri domin kinsah ran lada xakisamu. Dan haka dug abin dayataso mana a gd jemu muyi hkr murike sirinmu Allah xaikawo mana mafuta insha Allah
.
______________________________
★JAGORORIN SHIRIN SUKA CE: Shin kuna ganin qarancin ilimi da jahilci shike haifar da iyaye mata ke shiga sha’anin auren ‘Ya’Yan su ??? ↓↓↓
.
_____________________________
→Manana Abdul Aisha tace: Assalamu alaikum .
Ni kuwa a ganina ilimin akwashi aiki dashi ne ba ayi,anfisa boko agaba wai wayewa da neman yanci baza a taba mata yarta tayi shru ba Ayy kuwa ba aga dai dai ba tunda anki bin dokar Allah, Allah ya shirye mu ya gafarta mana.
.
_____________________________
→ Maman Zee tace: Assalamu alaikum,eh to yanasawa da kuma rashin godiyar Allah da kuma zamani da yaxo da wata wayewa wadda bata haddasa komi se lalata tarbiya.
.
_____________________________
→Ummu Nusaiba tace: Assalamu Alaikum Wannan hkne amma wata rana kuma harda kwadayin iyaye su bada yar su suna tsammanin zasu samu abin duniya daga baya kuma sai suga ba haka ba.
.
______________________________
→ Maman ilham tace: Ba karanci ilimi bane, rashin aiki da ilimin ne da kuma San zuciya.
.
_______________________________
★ JAGORORIN SHIRIN SUKA CE: Hanzari ba gudu ba shin bakwa ganin ‘Ya’yan suna da laifi wanda har yake kaiwa ga Iyayensu Mata sun shiga cikin sha’anin auren su har da qoqarin raba auren ??? ↓↓↓
.
______________________________
→Imranat Ado Bello tace: Gaskiyane galibamma sunfi laifi dan kuwa da suna yin haquri suna boye wani sirrin nasu da mazajensu dabasu sami wannan matsalolin da harzai kaisu ga saki.
______________________________→Ummu Nusaiba tace: Assalamu Alaikum Wannan hkne amma wata rana kuma harda kwadayin iyaye su bada yar su suna tsammanin zasu samu abin duniya daga baya kuma sai suga ba haka ba.
.
______________________________
→ Maman ilham tace: Ba karanci ilimi bane, rashin aiki da ilimin ne da kuma San zuciya.
.
_______________________________
★ JAGORORIN SHIRIN SUKA CE: Hanzari ba gudu ba shin bakwa ganin ‘Ya’yan suna da laifi wanda har yake kaiwa ga Iyayensu Mata sun shiga cikin sha’anin auren su har da qoqarin raba auren ??? ↓↓↓
.
______________________________
→Imranat Ado Bello tace: Gaskiyane galibamma sunfi laifi dan kuwa da suna yin haquri suna boye wani sirrin nasu da mazajensu dabasu sami wannan matsalolin da harzai kaisu ga saki.
______________________________
→ Maman ilham tace: .kwarai kuwa, domin baikamata ‘yar uwa tana daukan zantukan gdnta zuwa ga iyayentaba, kamata yayi tana hakuri da Lamuran ,domin ‘yar uwa tana iya mance dukkan wani abu da miji yamata sukuwa iyaye suna rike dashi, abu muhimmi shine tana hakuri da yafiya
.
______________________________
→ Aisha Imam tace: Sosaima yayanma sune ummul aba,is isin Kawo lalacewan wannan lamarin tunda inbasuzou sungaya abinda kestakaninsu damazajansuba su iyyayan bazasusan me,akecikiba dafatan zamu zama iyyaye nagari masusan farincikin yayanmu
.
_____________________________
★JAGORORIN SHIRIN SUKA CE: ‘Yan-uwa masu albarka wani qira, Nasiha, shawara zaku isar ga ‘Yan uwa mata masu saurin kai qorafin mazajensu wajen iyayensu ??? ↓↓↓
.
_____________________________
→Ummu Nusaiba tace: Ita dai mace a kullum Yakamata tasa aranta cewa komai take aljanar ta take nema kuma tasani Aljanna ba a samun ta asauki kuma Duk jarabawar dakika tana samunki adakinki kiyi hkr ki kuma tuna akwai wacce take da matsalar da tafi taki kuma ki kiyaye kai qara musamman wurin iyaye don wata uwar ko labari kibata zata riqe abin kuma tayi ta kallon mijinki da shi ki daure ki cije ki koyi riqe sirrin ki Allah yabamu hkr da kuma cin kowace irin jarabawa ta gidan aure.
.
Kuma Kisa addu a a gaba domin itace maganin kowace damuwa.
.
Allah yasa mu dace.
.
______________________________
→Haifa’u Bashir tace: Shawara dai itace Su rinka kokarin kauda matsalar a tsakaninsu kafin takai ga iyaye domin wasu iyayen zasu iya daukan zafi har yakai ga rabuwar aure.
.
______________________________
★ JAGORORIN SHIRIN SUKA CE: ‘Yan-uwa masu albarka wani qira Nasiha, shawara zaku isar ga iyaye musamman iyaye mata game da shiga sha’anin auren ‘Ya’yansu har yake kaiwa sun janyo musu saki awajen mazajensu ??? ↓↓↓
.
_______________________________
→ Ummee Zaria tace: shawaranmu shine iyaye su ji tsoran ALLAH subar ‘ya’yan suyi zaman aure kuma sudinga yi musu nasiha na alkhairi domin duk uwar da take bawa yarta shawaran alkheri tanada nasara.
.
______________________________
→Sameerah Aliyu Abdulmalik tace: Assalamu alaikum, shawara ta ga iyaye, susani aure ibadane sanna kuma karsu zama masu koyi da shaidan me raba aure.
.
_____________________________
→Ummu Aliyu Zariya tace: Iyaye mata ya kamata su nunama yayansu hkr da juriya. Susani su masuyin tarbiyace kada subari ‘baraka tafito akan abun da baitaka kara ya karyaba.
.
______________________________
→ Maman ilham tace: Iyaye yakamata suja girmansu, sudaina shiga harkar ‘ya’yansu, Koda ‘ya’yansu sunkawo musu korafi kamata yayi suyi musu nasiha tare da kwabar ‘ya’yan Akan Suna hakuri ba komi ake Kai karaba, ciki badan abinci kawai akayishi ba.
.
_______________________________
Kad’an kenan daga cikin Abunda Matan Zauren suka ce dan gane da wannan topic d’in, A lura cewa ba dukkan tattaunawar muka d’auko ba.
.
ALLAH Ya sanya Alkhayri acikin wannan Tattaunawar Ya kuma bamu ikon amfana da abunda muka tattauna akai (Ameen)
2017-12-28 19:14 (edited 2017-12-28 21:58 by ibnhujjah ) · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 30 user
This Week : 30 user
This Month : 983 user
Total all : 271249 visitors
LAST PAGES