Ring ring

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah Rubutawa Muhammad Ibrahim Bawa Maishinkafa
HAIHUWARSA
An haifi Sheik Dr Alhassan Saeed a wani gari da ake kira mekekiya a kusa da wani kauye da ake kira mai zuwo a karamar hukumar sule tankarkar a yankin Jigawa a shekarar 1956 iyayensa na daga cikin wadanda suka fara zuwa a garin
KARATUNSA
Malam ya fara karatunsa a kauyen dan kama duka a cikin karamar hukumar sule tankarkar amma sabida hali na rashin yarda da boko da dayawa daga cikin iyaye ke yi a wannan zamani yasa babansa ya cire shi daga makarantar ya maida shi makrantar allo a jobi cikin jihar Kano gurin wani malami mai suna malam Adamu jobi wanda a wannan lokaci babu wani malami kamarsa a wannan yankin, daga nan wani malami ya dauke shi zuwa jos inda ya hadu da wani malami mai suna malam Muhammad dan uwan malam Adam na jobi anan yaci gaba da karatu a gurinsa ya kuma ci gaba da karatun boko
A shekarar 1972 wani malami ya nemi da suje Maiduguri da suka je can ya haddace Alkur’ani a shekara guda daga nan kuma ya dawo jos yaci gaba da karatunsa a gurin wasu malamai daga cikinsu akwai
Malam Usman Misau
Malam Muhammad dan yayar mahaifiyarsa
Malam Audu alkalin shandam.
A1975 lokacin da gwamnati ta kirkiro universal basic education {UBE} malam ya fara karantarwa inda daga bisani ya daina karantarwa ya koma makaranta a shekara ta 1979 Arabic teachers college Katsina inda ya gama a 1984/85 ya fito da sakamako mai kyau wanda yafi na kowa a wannan shekarar har aka bashi kyauta.
A shekarar 1987 malam ya koma jamiar Ado bayero inda ya yi diploma a Hausa Arabic and Islamic studies bayan ya gama sai ya koma jamiar Jos inda ya yi digiri a Hausa Arabic and Islamic studies a shekarar da zai gama jamiar jos ne wasu larabawa daga kasar Saudia suka zo don shirya bita ga masu karatun addini malam yaje gaishesu sai suka nemi daya zo ya halarci wannan bita malam ya halarci bitan inda yazo na biyu sai larabawa suka ba shi shawara ya cike form don yin karatu a kasar Saudia anan ne ya yi digirinsa na biyu a tsangayar Alkur’ani.
Bayan ya gama digirinsa na biyu a kasar Saudia sai ya dawo jamiar Jos ya yi master nashi daga baya kuma a shekarar 2007 ya koma jamiar Usman dan Fodio ya yi PHD nasa
MATAYENSA DA YAYANSA
Malama yana da mata guda 4 da yaya 27 da jikoki daga cikin yayansa akwai
Abdulbsid
Mubarak
Adda’urrahman
Mujahid
Najib
Hamza
Kadija
Fa’iza
Basma
Rukayya
Ahmad
Maryam
Aisha
Yusra
Ibrahim
Aliyu
Umar
Majad
Mardiya
Fadl
Fudail
Muhammad da sauransu
MUAMALARSA DA YAN UWANSA DA SAURAN AL’UMMA
Malam ya kasance mutum mai kyakkyawar dabia ga yan uwansa da sauran al’umma da yake tare da su mutum ne mai hakuri da juriya bisa abun da aka mai inda za a mai abu na cutarwa kace zaka rama mai kokarin hana mutum yake yi yace a barsu da Allah
Malam ya kasance mai kyakkyawar muamala da sauran abokansa na da’awa duk wani abokin da’awa da suke tare da shi zaka samu yana fadan alakairi akansa domin sun san cewa mutum ne mai basira da hangen nesa, baya gaggawar bada fatawa akan addini akan abin da bai sani ba ni shaida ne a gabana an mai tambaya y ace bai sani ba a bari sai ya tambayi malamansa su ba shi amsa
GUDUNMAWARSA WAJEN KARANTAR DA AL’UMMA
Malam ya share rayuwarsa wajen karatu da karantarwa da yada sunnar Annabin rahama SAW ko a ranar da zai bar duniya saida ya karantar da littafin Atttargib Wattarhib na Imamul Munziri {karatun da yake ma take da hikimar safiya}
Malam ya rayu cikin Alkur’ani ya kuma koyar duk bayan sallar Asubahi ko Magriba in dai yana gari kazo kofar gidansa zaka Same shi yana karantar da Alkur’ani ko kuma yana karantawa.
Shine farkon wanda ya fara bude halka ta Alkur’ani a garin Jos a layin Mudi na Garba kusa da gidan malam Lawal Maka mutum sama da 500 sun haddace Alkur’ani gunsa.
Banan kawai malalm ya tsaya ba ya bada gudunmawa sosai wajen karantarwa wanda Allah kadai yasan yawansu daga ciki akwai
Shine shugaban kwamitin ilimi da ilimantarwa na kungiyar IZALA.
Shugaban mai bada fatawa na jama’atu JNI na jihar Plateau.
Mataimakin shugan shirya gasar musabakar Alkur’ani na jihar Plateau.
Ta sanadiyarsa aka gina shool for higher Islamic studies dake sarkin mangu wanda yanzu take hannun su sheik Sani Yahya Jingir .
Shine matashin ahlussunna na farko daya fara tafsirin Alkur’ani acikin a garin Kano a kofar gidan baba Iliya inda malam Aminu Ibrahim Daurawa ke karatu a yanzu lokacin sheik Ja’afar Mahmud Adam Allah ya jiknasa da rahama na ja mai baki {wannan magana shi ya fada mun baki da baki a kofar gidansa}.
Shine wanda ya fara kirkiro makarantar addini na mata sanda aka kafa kungiyar IZALA a yau dukwani makaranta na mata da aka bude a IZALA da sauran bangarorima malam nada sakamako na lada a ciki.
LITTAFAN DAYA KARANTAR A RAYUWARSA
Malam ya karantar da littafai da dama a rayuwarsa daga ciki akwai
Bulugul Miram
Riyadussalihin
Sahihul Bukari
Kitabuttauhid
Muwadda
Risala na Abi Zaidul Kairawani
Wasu littafai da suka shafi lugga
Attargib Wattarhib {ko ranar da zai bar duniya saida ya karantar da wannan littafi
RUBUCE RUBUCENSA
Malam ya yi rubuce da dama daga ciki akwai
Nasihatu dalibu li alimul arbab
Bidayatu dalib fi ilmul tajwid (wanda ake karantarwa a duk makaratun IZALA dama wasu makarantar musamman makaratun IZALA bangaren sheik Sani Yahya jingir (wannan shi ya fada mun baki da baki)
DALIBANSA
Malam yana da dalibai dayawa da suka yi karatu a gunsa daga cikinsu akwai
Malam Shehu Sulaiman {wanda ya wakilci Nigeria a gasar karatun Alkur’ani da aka yin a duniya a kasar Saudia}
Malam Sani Ahmad {yaje musabakar Alkur’ani na kasa da ake shiryawa a Usman dan Fodio}
Malam Ibrahim Idris darussa’ada
Muhammad Nuru Kalid {limamin masallacin yan majalisa dake apo Abuja}
DR Abdurrahman Idris {lecture a Aminu Kano Legal college for Arabic and Islamic studies}
Gwani Muhammad Adam Alkadi {dan London}
Malam Mika’il Muhammad Mika’il
Malam Salihu fari
Malam Ibrahim {abu farhan}
Malam Hashim Sani Hashim
Muhammad Kabir {qariu}
Malam Sani Ahmad {abu Rukayya}
Sai ni ni mai rubutu wanda a makarantarsa na fara koyon hada baki da sauran dalibai masu tarin yawa
MUTUWARSA
Malam ya mutu ranar laraba {ranar da amininsa sheik Ibrahim Bawa mai shinkafa ya rasu} 08-07-1438 / 05-04-2017 yana da shekaru 61 a garin Kano shugaban kungiyar IZALA sheik Imam Abdullahi Bala-lau ne ya mai salla dubbannin al’umma ne suka halarci janazarsa daga Nigeria da wajajen Nigeria
Allah ya jikansa yasa Aljanna ce makomarsa
Abu Aisha Muhammad Ibrahim Bawa Mai shinkafa
2018-03-04 05:20 (edited 2018-03-04 06:09 by ibnhujjah ) · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 27 user
This Week : 209 user
This Month : 451 user
Total all : 270717 visitors
LAST PAGES