Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah img

Kamar yadda ka sani masu amfani da wayar android suna fama da irin wannan matsala na bude data da kanta batare da ka budeba, irin wannan matsalar tana 6atawa mutane rai haka kawai ka rufe datar wayarka bayan wani dan lokaci kawai saika tarar ta bude kanta idan ta bude kuma idan wayar da mb ko kudi nan take zakaga wasu apps din sun bude kansu suna amfani da mb ganin data ta budu sukuma apps sai suyi ta aiki sannan idan data tana bude wayar zakaji tana daukan zafi kokuma ta dingama wani shirme na banza, to irin wannan matsalar Malware ne yake kawo irin wannan matsalar ita kuma malware, yawan janye janye wato download na kowane irin apps ko game suke suke kawato malware da kuma yawan Ture ture ta Xender sabo da wasu apps din suna zuwa da matsala to yawancinmu bama sanin hakan sai kawai da zarar munga apps masu kyau batare da wani dubawaba kawai saimu bukaci wannan apps din har a turo mana ko muyi download nasa, sannan idan muka samu apps din bama lura da permision na app din yayin Install kawai nan take sai muyi install bayan sukuma app din suna bada permision yayin da kake install kan cewa apps dinnan yana da kaza kaza amma bama lura da wannan saide kawai mu amince da abin da suka fada sai kuma daga baya app din sai yazo ya jazawa wayarka matsala, ta dingama abubuwa marasa dadi marasa amfani ka kasa gane matsalar wayar har kanaji wayar ta fita daga kanka, data ta dinga budewa da kanta wayar tana wani kakkamewa tana makalewa tana wani ciccijewa hada dasu daukan zafi da sauran matsaloli,
Duk irin wannan matsalar Malware ce take janyosu ita kuma malware na fada maka abin da yake janyota sannan idan kuma malware tayi yawa a wayanka to cikin kankanin lokaci wayarka zatayi break kokuma taci file ta yadda wayar bazata ta6a amfaniba harsai an chanja mata file an dora mata wani sabo sannan zatayi amfani shikuma chaja file yana da dan tsada,
Dan haka tun kafin wayarka takai ga wannan matsalar gara kasan yadda zakayi kafin wayarka takai ga hakan, dan haka ga yadda zakayi
Da farko kayi Restore All na wayar taka, bayan kayi Restore din
sannan kaje google kayi download na wannan app mai suna MALWARE BYTE.apk
Kokuma ka shiga wannan link din ka daukoshi kai tsaye
Download Apk
Bayan ka sauko da wannan application to yanzu sai kayi install dinsa sannan ka dubeshi idan ya bude zakaga ya fara Cheack Device Issues idan yadan jima zakaga ta nunoma Your device has issues
To karka damu kawai ka duba kasa zakaga Fix Now saika danna nan bayan ka danna zata danyi seach kadan idan ta gama zata nuno wani shafin to a shafin saika duba kasa ka shiga Inda aka Rubuta
Run Full Scan
Da zarar ka shiga nan take zakaga wayar ta fara Scanning shikkenan saika jira nan wani lokaci har saita gama, zata dan dauki lokaci kadan kafin ta gama da zarar ta gama shikkenan, saika fito
Yanzu wayarka tayi nomal babu wani matsala akanta zakaga ta koma kome nomal data zata dena bude kanta sannan duk wani malware dayake kanta ta fitar dashi shikkenan sai kaci gaba da amfani da wayarka cikin kwanciyar hankali,
Amma idan kadan samu lokaci sai kana komawa cikin app dinnan kana yiwa wayar scanning domin tabbatar da lafiyar wayarka
Allah ya bada sa,a
2018-02-07 18:09 (edited 2018-02-07 18:47 by ibnhujjah ) · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 8 user
This Week : 22 user
This Month : 9 user
Total all : 270275 visitors
LAST PAGES

pacman, rainbows, and roller s