Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah ZA MU IYA AURAWA KANWARMU DAN SHI'A ? Tambaya : Assalamu'alaikum..da fatan malam yana lafiya.. Malam wata kanwarmuce ta kamu da son dan shi'a dake ungurmu kuma munyi kokarin rabasu saboda wasu daga cikin munanan dabi'ar su kamar zagin sahabbai, mutu'a, zagin matan annabi da dai sauransu. Amma abin dai ya gagara. Sai dai ya tabbatar mana da cewa shi tinda aka halicce shi bai taba aikata wadan nan laifukan ba. Sannan kuma bai yarda da hakan azuciya ko a baki ba. Illah iyaka yasan yana bin zakzaky ne akan yana kiran hadin kai ga musulmi. Shi iya wannan ne ya amsa amma ya barranta ga duk wani munmunar akidar shi'a. A iya zaman da mukayi dai bamuga yana aikata wani kaba'irar ba dan a masallan mu yake sallah tin tashin mu dashi. Shin malam ya halatta mu bashi. Ko kada mu bashi. Amsa: To dan'uwa tabbas a cikin addinin shi'a akwai manyan abubuwa wadanda suke warware musulunci: 1. Daga ciki akwai zagin mafi yawancin sahabbai, tare da cewa, Allah ya tabbatar da cewa ya yarda da su a ayoyi da yawa a cikin alqu'ani, duk wanda ya ce mafi yawancin sahabban Annabi s.a.w. sun kafirta tabbas ya karyata Allah, wanda ya karyata Ubangiji hukuncinsa a fili yake. 2. Yana daga cikin akidunsu tabbatar da cewa : Alqur'anin da yake hannunmu bai cika ba, tare da cewa : Allah ya tabbatar : zai kiyaye shi, har abada. 3 . Rafidha 'yan shia sun tafi akan cewa Nana A'isha Mazinaciya ce, tare da cewa Allah ya kubutar da ita daga abin da munafukai suka zarge ta da shi a ayoyi guda goma a suratun Nur. Duk da cewa da yawa daga cikin 'yan shi'a suna kore wadannan aqidu, saidai ayyukansu da littatatafansu da maganganunssu, suna karyata korewarsu. Shugabansu Zakzaky yace ba ya zagin sahabbai, kawai sai muka gan shi a zaune a Husainiyyar Zariya yana la'antarsu, Haka Yakubu Yahya na Katsina shi ma ya yi ikrarin haka, sai ga shi mun ji shi yana siffanta Sahabbai da 'yan PDP, yana ci musu mutunci da cewa sun yi juyin mulki. Ya wajaba ka sani yana daga cikin manyan aqidun 'Yan shi'a TAKIYYA wato yin karya ga wanda ba dan shi'a ba, kuma duk wanda bai iya wannan ba, to bai cika dan shi'a ba a wajansu, domin ginshikin addininsu ce, don haka kar ka dogara da maganarsa. Annabi s.a.w. yana cewa : "Idan wanda kuka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura masa" kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1084, duk wanda addininsa ya kunshi abin da ya gabata, bai halatta a aura masa mace ba, tun da Allah bai yarda da hakan ba, kuma addininsa ba yardajje ba ne, Allah ya ba ta miji nagari wanda ba dan shi'a ba. Allah ne mafi Sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
2018-02-06 17:58 · Reply · (0)
* ibnhujjah * ibnhujjah Tambaya*
Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh, malam mutum ne yarasu yabar dubu 300,000,yabar yara biyar 4 maza da Mace daya,ya rabon gadon su yake?mungode
*Amsa*
Wa alaikum assalam
Za'a bawa kowanne namiji )66,666(, macen kuma sai a bata )33,333(.
Akwai naira uku da za ta ragu, da fatan za su yiwa juna afuwa ko kuma su bawa wanda ya raba musu gadon.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
2018-02-06 17:59 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 20 user
This Week : 576 user
This Month : 818 user
Total all : 271084 visitors
LAST PAGES

Snack's 1967