XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah ZAN IYA BADA ZAKKA BA TARE DA NA SANAR CEWA ZAKKA CE BA ?
Tambaya:
Tambaya ce daga wata 'yar uwa kamar haka: "Akwai Marayu a karkashi na,kuma dukiyarsu Rana tare dani,ina ririta musu bana son taba ta,musamman asalin dukiyar. Yanzu haka sai iyayena suka nemi na bawa daya daga cikin 'yan uwa rancen kudi don yaja Jari. Yanzu haka an fitar da Zakkah daga kudin marayun,shine nake so na bashi amma ba bashi ba. Sai dai in nace Zakkah ce, to su iyaye na bazasu fahimci dole ne ko an sami hasara dole ne a fitar da zakkah ba,zasu kara tattaro matsaloli suce a bada kudi akansu. Shin ina iya bashi kudin ba tare da nace Zakkah bace, la'akari da matsalolin da fadar Zakkar ce zai jawo min???? Allah ya karawa Malam ilimi da ikhlasi.
Amsa :
To 'yar'uwa Allah madaukaki ya yi umarni da kiyaye dukiyar maraya, da kuma hana cinta, in ba da gwargwadon bukata ba, ga wanda yake talaka, kamar yadda ayoyin farko-farkon suratunnisa'i suka tabbatar da hakan.
Ba shi daga cikin sharadin zakka, sai an sanar da wanda aka bawa cewa zakka ce, kamar yadda Ibnu Khudamah ya yi bayanin hakan a littafinsa Al-mugni 28 da kuma Annawawy a littafinsa Al-majmu'u 63, don haka in kika bawa fakiri da niyyar kin fitar da zakka ko da ba ki sanar da s hi ba ta yi.
Saidai malamai sun hana yin dabara wajan bada zakka, kamar ya zama kana so ka yi ma mutum kyauta, amma maimakon ka dauki kudinka ka ba shi sai rowa ta hana ka, sai ka yi dabara ka ba shi zakkar da ka yi niyyar fitarwa.
Duk mutumin da ya bayar da zakka yadda Allah ya yi umarni, tabbas Allah zai mayar masa da ninkin-ba-ninki.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
2018-02-23 22:31 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 14 user
This Week : 70 user
This Month : 158 user
Total all : 270424 visitors
LAST PAGES