Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah ZANGA ZANGAR SHUGABANNIN KIRISTOCIN NIGERIA:
1. Allah wadaren halayyar da shugabannin kungiyar kiristocin Nigeria take nunawa na rashin dattako, da rashin yarda da hakkin da Musulmi ke da shi na mulkar Nigeria.
2. In ba ku manta ba babu irin barnar da ba ta faru ba a lokacin mulkin Goodluck Jonathan na shekaru shida a Nigeria; kama daga irin yadda yan ta'addan bokoharam suka mamaye manyan garuruwa a Nigeria, kuma suka hana Jama'a sukuni a garuruwan da ba su mamaye ba, har zuwa irin kashe-kashen da yan fashi, da barayi suka yi ta yi a jihohi daban daban, ina tunawa a ranar 5/4/2014 an yi jana'izar mutane 120 a lokaci guda wadanda yan fashi, da barayi suka kashe a kauyen 'Yargaladima cikin jihar Zamfara, har yau har gobe wannan labarin yana rubuce a cikin shafin sashin Hausa na BBC na rana 7/4/2014, to amma duk da irin wadannan balbalin bala'in da aka yi ta fama da su a kusan dukkan yankunan Nigeria babu inda shugabannin kiristocin Nigeria suka shirya zangazanga saboda yaye wa gwamnatin Goodluck Jonathan zani a kasuwa, a'a, sai ma irin abin da suka yi ya yi na kare ita gwamnatin Goodluck Jonathan din ido na ganin ido, babu tsoron Allah, babu kuma kunyar al'ummar Nigeria!
3. Shugabannin kiristocin Nigeria mutane ne marasa kunya, mara kara, wadanda zukatansu ke cike da kiyayya ga al'ummar Musulmi, wadanda suke kasa sukuni da hutun zuciya a duk lokacin da aka ce wani musulmi ne shugaban Kasar Nigeria; Wannan shi ne ya sa yanzu suke ta shirya zanga zangar kware wa gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari zani a kasuwa tsammaninsu hakan zai sa ya fadi zabe a shekarar 2019!!
4. Abin da shugabannin kiristocin Nigeria suke mantawa, ko kuma suke jahilta da gangan shi ne: na daya: su fa kiristocin Nigeria minority ne idan aka gama su da musulman Nigeria. Na biyu: shugaba Buhari bai ci zabe da kuri'un kiristocin Nigeria ba, a'a kuri'un kiristocin Nigeria da ya samu ba su wuce kuri'u irin na hana rantsuwa ba, wannan hakika dukkan masu lura da yadda al'amura ke tafiya cikin Nigeria suna sane da ita.
5. Muna kira ga Shugaban Kasa da kada ya damu da irin wannan hayaniya wacce take cike da kauyanci, da hassada da shugabannin kiristocin Nigeria ke yi; domin neman tsorata shi, da kauda hankalinsa daga gina Nigeria domin fa'idantar al'ummarta ta yanzu da kuma wacce take zuwa nan gaba.
6. Lalle mu al'ummar Musulmin Nigeria muna nan muna bibiyar wannan sakarci, da hayaniya da shugabannin kiristocin Nigeria ke yi cikin wadannan kwanaki, kuma lalle muna da wayayyen martani da za mu iya mayarwa a lokacin da ya dace.
Allah Ya taimake mu Ya ba mu lafiya da zaman lafiya har kullum. Ameen.
Dr Ibrahim Jalo Jalingo.
2018-05-23 18:35 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 24 user
This Week : 47 user
This Month : 70 user
Total all : 270253 visitorsUnited States
LAST PAGES

Insane