XtGem Forum catalog

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah Dattin Zina

Zina wata irin dau'da ce wacce idan ta kama zuciyar 'dan Adam tana da wuyar wankuwa.. Kuma ko da ta wanku, batta wankuwa gada daya sai kaga gurbinta yana nan.

Duk zuciyar da ta riga ta chudanya da Zina, ta zama zuciya mai Ha'inci. Kuma ma'abocinta ba zai ta'ba zama cikakken mumini ba. Sai dai idan ya tuba.

Bincike ya nuna cewa NAMIJI idan yayi nisa acikin Zina, har zuciyarsa takan kawo masa sha'awar yi da muharramansa ma. Kamar Uwarsa wacce ta haifeshi, ko dangin Uwarsa, ko dangin Ubansa, ko Qannensa mata... Wani lokacin zuciyarsa takan jefa masa sha'awarsu.

Hakanan Mace idan ta zama Mazinaciya, babu wani Minti guda acikin rayuwarta fache ta tanadeshi ne domin aikata zina ko kuma aikat duk abinda zai ja hankalin mazinata 'yan uwanta.

Zina mugun ciwo ne wanda yakan kashe mutum ta ciki, tun kafin ya kasheshi ta waje.

Wannan yasa Manzon Allah (saww) yace "MAI ZINA BA MUMINI BANE SHI, YAYIN DA YAKE ZINA".

Awani hadisin kuma ya lissafta TSOHON MAZINACI acikin mutanen da ba zasu shiga Aljannah ba.

Zina idan tayi nisa azuciyar mutum, takan lalata mafiya yawan zuriyarsa.... Koda bayan ransa sai. Kaga ana samun yawaitar masu koyi dashi acikin zuriyarsa.

'Yan Uwa. Mu nisanci ZINA kuma mu nisanci duk masu yinta... Domin ita dabi'a takan yi naso ne.

YAYI ZINA DA MATAR AURE!!

Assalmu alikum malam. Don Allah a sakaya sunana. Malam don Allah ayi kokari duk abinda na fada a wallafa shi a wannan zauren mai albarka don ya zama darasi garemu baki daya.

Ni dai ma'aikacine kuma yanzu haka ina wata jiha don aiki kamar yadda daga lokaci zuwa lokaci aiki yakan kaini. Zuwata wannan jihar sai na hadu da wani abokina har ya zamanto banda wurin fira sai wurinshi.

A nan wata rana na hadu da wata yarinya inda daga karshe dai na karbi lambar wayarta. Hira tsakanina da yarinyar nan ya wuce na tsakani da Allah daga karshe har sai da muka yi zina (Astagrirullah wa atubu ilaihi).
Kafin wannan mummunan abin ya faru, abinda na iya sani a game da yarinyar daga wurin abokina shine; ta taba aure amma mijin ya gudu ya barta ba a san inda yake ba, kusan shekara daya kenan amma yanzu kotu ta raba auren wand ita ko da wasa bata taba fada min hakan ba. Sai dai cewa tayi tana da saurayi amma ya yaudareta ya gudu ya barta.

Mun ci gaba da abinda dani da ita muka kira soyaiya duk da cewa wallahi har cikin zuciyata ni na san bana sonta sai dai ban san abinda ke cikin nata zuciyar ba.

Kada dai in tsawaita wannan labarin, daga karshe dai ranar wannan sallan babba sai ita da kawarta suka kawo mini abinci sai naji a zuciyata kuma yanzu babu wanda hankalina ya karkata wurinta sai kawar. A dai dai wannan lokacine ita yarinyar take cemin zata yi tafiya zuwa wani wuri amma ba zata dawo ba sai bayan wata daya.

Bayan ta tafi sai na koma kiran ita kawar a waya wanda daga baya na samu hadin kanta da sunan soyaiya. Cikin irin firar da mukeyi ne, ita kuma don ta samu gindin zama sosai a zuciyata ta fada min abinda shine dalilin tashin hankalin da bana taba shiga ba. Watau abinda ta fada min shine. Ko na san cewa wannan yarinyar tana da aure? Nace wallahi ban sani ba. Kuma hakane wallahi ban sani din ba. Abinda na sani shine an kashe aurenta da mijinta da ba a san inda yake ba.

Tafiyar nan da take cewa tayi zatayi wata daya a wurin ashe gidan mijinta ta koma. Kuma duk da cewa ta koma gidan mijin tana kirana kuma muna waya har da maganganu na batsa. Amma ban san cewa a gidan mijin take ba.
Allah ya gafarta malam. A daidai wannan lokacine nake baran addu'a a wurin yan uwa, ubangiji Allah ya yafemin wannan abinda na aikata. Lallai wannan ya zama dalilin tuba a gareni. Kuma ina mai tuba zuwa ga Allah. Ina son wannan abin ya zamo darasi ga kowa. Maza da mata, muji tsoron Allah.

Shin ko Allah zai karbi tubata? Sannan kuma malam wadanne irin addu'o'I ya kamata in rika karanta wa don tuba da neman yardar Allah. Ina cikin tashin hankali wanda ban taba shiga cikinsa ba a rayuwata.

Allah kadai yasan halin da nake ciki har a yanzu da nake wannan rubutun.
(Al'ameen)

AMSA
******
Tabbas kayi katobara, ka zalunci kanka. Ka aiwatar da Babban Kaba'ira.

Amma babban abinda ya bani haushi kuma ya bani mamaki acikin wannan dogon labarin naka shine:
Wato kai ba wai kana yin nadamar aikata Zina bane. A'A. Kai kana yin nadama ne kawai saboda ance maka matar aure ce!!!

Agaskia dunia ta rudeka. Kuma shaitan ya riga ya rinjayeka. Ka zama nasa.

Kuma tabbas mazinata suna haduwa da Qaskanci da wulakanci da Qaskanci da talauci tun daga nan dunia kafin aje lahira.

Don haka ka tuba izuwa ga Allah. ka kaurace ma zinan da kakeyi. Kuma ka dena duk wata hulda tare da abokananka wadanda kuke yin zinar nan tare..

Ka yawaita istighfari da aiyukan alkhairi wadanda Allah yake kankare Zunuban bayinsa dominsu. (Kamarsu azumin nafila, tasbihi da salatin Annabi saww.)

Sannan kaje ka nemi gafarar mijinta domin shiga hakkinsa da kayi. Idan kuma neman yafewarsa zata janyo maka tozarta da kuma tashin hankali, to sai kaci gaba da yi masa addu'a. Kana nema masa gafara awajen Allah.

​ZINA DA KANIN MIJI (SUBHANALLAH) 

ASLM  Mallam na samu matsala ne a rayuwata   ina zaune da mijina shekaranmu 7 da aure akwai kaninsa da yake bibiyata malam tun bana kulashi har ya kai yenzu har yakai muna wasa dashi.

Nayi nayi ya bari yaki bari. mai ya kamata inyi?

Har ya saba inya shigo ya danneni har sai ya biya bukatansa akaina kuma bana iya che masa komai. Malam ataimaka mun da addu’oi da shawarwari.
AMSA

*******

Wa alaikis salam. 

Hakika kin aikata kuskure babba. Domin kuwa bayan shirka babu wani zunubi mafi girma awajen Allah kamar zina. 

Manzon Allah (saww) yace : “MAZINATA ANA HURA MUSU WUTA NE BISA FUSKOKINSU (RANAR ALKIYAMAH KENAN). 

(Imam Tabaraniy ne ya ruwaito). 
Sannan acikin hadisai da dama Manzon Allah (saww) ya bayyana cewar Akwai wani ruwa mai bala’in doyi wanda ke fita ta farjojin Mazinata acikin Wuta. Wannan ruwan dashi ake yiwa sauran ‘yan Wuta Azaba. 

Sannan acikin wani Sahihin hadisi wanda Imamul Mundhiriy ya ruwaito acikin Targheeb wat-Tarheeb, Manzon Allah (saww) yace: “ALLAH YANA KUSANTOWA GA BAYINSA, SAI YAYI GAFARA GA DUK MAI NEMAN GAFARA. AMMA BANDA MATAR DAKE ZINA DA FARJINTA…. “.

Ya zama wajibi kiji tsoron Allah ki dena domin kuwa wannan laifin zai iya janyo miki bala’i da tozarta da wulakanta dake da danginki da iyayenki tun daga nan duniya. Aranar lahira kuma Farjin naki da kike zinar dashi, da kuma sauran gabobin jikinki sune zasu tona asirinki agaban Zatin Allah, ga dukkan halittu suna kallonki. 

Zata yiwu ki samu ciki ta dalilin wannan Zinar, kuma ki shigo ma mijinki da wannan cikin (Ma’ana ba zai gane cewa cikin ba nasa bane). Alhali Manzon Allah (saww) yace:

“DUK MATAR DA TA SHIGO MA WASU MUTANE DA WANI WANDA BA CIKINSU YAKE BA, TO ITA BA KOMAI BACE AWAJEN ALLAH. KUMA (ALLAH) BA ZAI SHIGAR DA ITA ALJANNARSA BA… “

(Nisa’iy hadisi na 3481, Abu Dawud Hadisi na 2263).

Shi kuwa wannan Qanin Mijin naki yaci amanar Allah da Manzonsa (saww), Kuma yaci amanar ‘Dan uwansa (wato mijinki). Kuma yana daga cikin mutanen da Allah yake yin tsinuwa agaresu. 

Manzon Allah (saww) ya gaya ma Sahabbansa cewa “WALLAHI MUTUM YAYI ZINA DA MATAYE GUDA GOMA, SHI YAFI SAUKI AGARESHI (WATO SAUKIN AZABA AKANSA) FIYE DA YAYI ZINA DA MATAR MAKOBCINSA”.

(Imamu Ahmad da Tabaraniy ne suka ruwaitoshi). 

Acikin riwayar Ibnu Abid dunya kuma daga Sayyiduna Abdullahi ‘dan Umar (ra) : “WANDA YAYI ZINA DA HALAL DIN MAKOBCINSA (WATO MATAR MAKOBCIN KO KUYANGARSA) ALLAH BA ZAI DUBESHI BA ARANAR ALQIYAMAH (WATO BA ZAI MASA KALLON RAHAMA BA) KUMA BA ZAI TSARKAKESHI BA. KUMA ZAI CE MASA “SHIGA WUTA TARE DA MASU SHIGARTA)”.

To in dai haka lamarin yake akan matar Makobci, to yaya kuma matar ‘Dan uwa?? 

Saboda guje ma faruwar irin wannan Fasadin shi yasa Manzon Allah (saww) yace : “KADA WANI MUTUM YA KEBANCE TARE DA WATA MACE, FACHE SAI TARE DA MUHARRAMINTA”.

Sai wani yace “Ya Rasulallahi shin Makusancin Miji fa?”. 

Sai Manzo (saww) yace “MAKUSANCI AI SHINE MUTUWA” (Wato shine yafi ‘barna kenan). 
Abinda zakiyi shine :

– Da farko ki tuba zuwa ga Allah ki janye jiki daga wannan kwarton fasikin dake zuwa miki. 

– Ki hanashi shigowa amma idan bai hanu ba, Ki sanar ma mijinki cewa lallai ya hana wannan Qanin nasa shigowa inda kike. 

– Ki rika tuna lahirarki da kuma tsayuwarki agaban zatin Allah. Da kuma kusancin Allah gareki ako yaushe. 

– Ki sani cewa Biyan bukatar Sha’awar Minti biyar zata iya janyo miki Wulakantar duniya da lahira. 

– Ki tuna rayuwar yaranki da kuma tarbiyyarsu. Kuma ki dubi amanar Mijinki da kike ci. 

Ki Yawaita Istighfari da Azumin nafilah domin samun tsarkaka daga wannan alfashar. 

– Idan Mijinki ba mazauni bane, gara ki matsa ki bishi wajen da yake aiki ku zauna achan domin samun tsira da Imaninki da mutuncinki. 

– Ki rika yin wannan addu’ar domin nisanta kanki daga alfasha : “ALLAHUMMA JANNIBNEE MUNKARATIL AKHLAQI WAL AF’ALI WAL AHWA’I”.

Allah ya sawwake ya gafarta miki ya shiryeki tlya tsamoki daga kowanne laifi, tare damu baki daya. 

WALLAHU A’ALAM. 

HANYOYI 14 DA ZAKA BI DOMIN GUJEWA AIKATA ZINA:

Babban Maganin da zai hanaka yin Zina, shine:

1. Tsayuwa abisa tafarkin Allah da Manzonsa (saww) da gaskiya.

2. Cikakken jin tsoron Allah afili da boye. 

3. Kulawa da yin Sallah akan lokaci, kuma acikin Jam’I. Tare da neman ilimin sanin Sallar.

4. Zikirin Allah safe da yamma tare da neman tsarinsa daga Sharrin Shaitan ako yaushe.

5. Tuna girman Allah da kuma Kusancinsa gareka/gareki.

Yana tare dakai/dake alokacin da kuke aikata wannan Kaba’irar

 6.Tunowa da girman azabar da Allah ya tanadar ma MAZINATA alahira.

7. Tunowa shaitan da kuma kaidinsa da yake Qullawa domin hallakar da ‘Yan Adam.

8. Gujewa kadaituwa da duk wata Matar da ba Muharramarka ba/ko Namijin da ba Muharraminki ba.
9. Kaucewa kalle-kallen fina-finan batsa. Ko kuma wakoki da hotunan batsa.

10. Kaucewa abota ko Qawance da duk wani saurayi Mazinaci ko budurwa Mazinaciya.

11. Ka tuna cewar Wannan da zaka yi zinar da ita: 

‘diyar wani ce, Qanwar wani ce, Yayar wani ce.

Watarana kuma zata zama Uwar wani.
To yadda kayi Zina da ita, kaima sai anyi Zina da Uwarka, ko Qanwarka, ko yayarka, ko ‘yar da ka haifa.

12. Addu’ar neman tsari daga Miyagun ayyuka, da mummunan tunani.

“Allahumma inni a’uzu bika min Munkaratil Akhlaaqi wal Af’aali wal Ahwa’I.”

13. Daga karshe kuma ka tuna cewa zaka iya kamuwa da wata mummunar chutar da zata zamanto ajalinka.. Kuma koda baka kamu da Chutar zahiri ba, Wallahi in dai ka aikata zina sai chutar Munafurci ko Fasikanci ta shiga zuciyarka. 

14. Tuno ranar da za’a tsayar da kai agaban Allah, a ranar taron Alqiyamah.. Ga iyayenka da Kakanninka har Jikokinka da jikokin-Jikokinka.. agabansu al’aurarka zata bada shaidar cewa Ka aikata abu kaza da ita arana kaza, awaje Kaza.. Mala’iku kuma zasu kawoshi arubuce. 

Fatanmu shine Allah shi kiyayemu baki daya daga wannan mummunan aiki. Wadanda kuma shaitan ya riga ya rudesu, to Allah yasa wannan rubutun ya zama dalilin tubansu. 

KU KIYAYI ZINA

A’amash ya ruwaito daga Sufyan daga Huzaifah bn Alyaman (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:

“YA KU JAMA’AR MUSULMAI, INA GARGADINKU AKAN ZINA (KU NISANCETA). DOMIN ACIKINTA AKWAI ABUBUWA GUDA SHIDA :

GUDA UKU ADUNIYA, GIDA UKU KUMA A LAHIRA. AMMA WADANDA SUKE ANAN DUNIYA SUNE :

1. Gushewar Kwarjini. 

2. Dawwamammen Talauci. 

3. Gajartar rayuwa (Wato rayuwarsu ba zatayi tsawo ba). 
AMMA WADANDA ZASU RISKA A LAHIRA SUNE :

1. Fushin Allah. 

2. Mummunan Hisabi. 

3. Dawwama acikin Wuta. 

A duba littafi mai suna “Akhbarun Nisa’,  babin dake magana akan haramcin zina. 

Ya Allah ka kiyayemu daga aikata zina da dangoginta. Ka tsare mana Qannenmu da ‘ya’yanmu da Matanmu daga sharrin Zina da Mazinata. 

YA’DUWAR ZINA ACIKIN AL’UMMA

Acikin kashi na farko munyi magana akan illolin da ya’duwar zina take kawo ma al’ummah. Yanzu kuma in sha Allahu zamu duba muga wasu daga cikin dalilan da suka kawo wannan bala’i :

1. TALLE : Mafiya yawan yara Matan dake yawon talle acikin kasuwanni, Garejoji, Tashoshin Mota, da Unguwanni, suna cikin hatsarin afkawa cikin wannan mummunar dabi’a. Ba don komai ba sai saboda yadda kullum zasu rika jin kalamai na batsa da Kuma Miyagun wasanni irin na batsa da suke samu daga Shashashun samari da kuma tsofaffin ‘Yan tasha. 

2. WAYOYIN SALULA : Wayoyin Salula suna taka mummunar rawa cikin yaduwar fasadi da lalacewar tarbiyyar al’ummah. Musamman ta bangaren Hotuna da Bidiyo na batsa da recording na kalmomin batsa wanda Matasa maza da Mata suke turawa a wayoyinsu. 
Yara Qanana sukan kalli Hotunan yadda ake jima’i. Daga nan kuma sai Shedanci ya shiga zukatansu su fara tunanin hanyoyin da zasu bi su rika samun biyan bukatarsu,  alhali da chan irin wannan tunanin bai ta’ba shiga kwakwalwarsu ba. 

3. WHATSAPP : Ita ma kafar sadarwa ta whatsapp tana taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar al’ummah. Harma ta zarce Facebook ko Twitter. 
Domin kuwa a Whatsapp ne watsatsun Samari da ‘Yan Mata (har ma da wasu Matan auren) suke bude groups musamman don koyar da zina!!.
Ta wannan hanyar suke sabawa da juna har su rika haduwa da juna. Akwai ma Kungiyoyin Matan aure ‘Yan Madigo wadanda har auren juna suke yi. (Wal Iyazu bil Lahi). 

4. MAKARANTUN SAKANDIRE : Akwai Yara Mata da dama wadanda sun lalace ne tun a Makarantun Sakandiren kwana (Boarding Schools) ta sanadiyyar Malamansu dake tursasa musu suyi Zina dasu, Ko kuma su atsakanin Junansu su rika aikata madigo. 
Hakanan a bangaren Mazan ma wasu tun daga Sakandire suke zama ‘Yan Luwa’di ta hanyar yi da junansu ko da Malumansu. 

5. MANYAN MAKARANTU : Su ma wadannan sun zama manyan dalilan watsewa ga wasu ta dalilin chakuduwar jinsi (Maza da Mata awaje guda). 
Zaka ga har abota ake Qullawa atsakanin Mata da Maza. Sai kaga Matar aure ko Qatuwar Budurwa ta Qulla abota tsakaninta da wani Qato haka kawai saboda ajinsu guda. 
Hakanan munsha jin yadda wasu lalatattun lakcharori suke tursasa yara Mata wajen yin zina dasu saboda su basu Maki (Marks). 

6. FINAFINAI : Ya’duwar Fina-finai na waje da kuma na gida shima ya taimaka wajen watsewar al’amura. Ba don komai ba, idan ka lura da yadda rayuwar Matan hausawa take acikin shekarun 1980 zuwa 2000 Zaka ga ba daidai take da wacce mukeyi yanzu ba. 

Tun daga salon Dinkunan da suke sanyawa, da kuma yadda suke kula da tarbiyyar yaransu, da kuma biyayyarsu ga Mazajen aurensu. 

7. WURAREN PARTY : Idan akayi la’akari da yadda kullum harkokin Party suke Qara bunkasa atsakanin Matasa da kuma irin watsewar da akeyi awajen, lallai za’a fahimci cewar Harkar Party tana daga Miyagun abubuwan dake addabar tarbiyyar al’ummah.
Ana haduwa Maza da Mata awajen kuma ana aikata haramtattun abubuwa iri-iri wadanda ba sai na lissafa ba. 

8. HIRAR ZAMANI : Hira irin ta Samari da ‘Yan matan Zamani itama babbar jigo ce wajen yaduwar Zina. irin wannan hirar ta bambanta da wacce akeyi a shekarun baya – 
– Kadaicewa da juna (Haramun ne). 

– Ta’ba jikin Juna (Haramun ne). 

– Zuwa Dakin Samari (Haramun ne).

– Hirar Batsa. (Haramun ce). 
To wannan ka’dan kenan daga abubuwan dake faruwa a sakmakon hirar nan irin ta Matasan zamani. 

9. MIYAGUN SUTURA : Miyagun suturar da Matan zamanin nan ke sanyawa wanda ke bayyanar da siffar jikinsu, ita ma babbar musibah ce wacce ta Qara habbaka ya’duwar zinace-zinace. Ba don komai ba, sai yadda hakan ke Qara janyo hankulan Wasu Mazajen da kuma Motsa Haramtacciyar sha’awa a zukatansu. 
A Kauyuka abin da sauki-sauki. Amma a birane zaka ga har Matayen aure masu manyan Yara ba’a barsu a baya ba. (Allah shi kiyaye). 
Ya Allah albarkacin wannan Wata na Ramadhana da Alqur’aninka wanda ka saukar acikin watan, da kuma wanda ka girmamashi da Alqur’ani, Ka yaye mana wadannan matsalolin, Ka tsarkake zukatanmu ka tsaftacemu daga dukkan alfasha don falalarka da rahamarka. Ameeen. 

 nayi bayanin wasu manyan dalilan dake janyo ya'duwar zina acikin al'ummah sai dai nayi babbar mantuwa. Na manta da wanu babban dalili. Wannan ba komai bane illa : Dogon Karatun Boko.

Da yawa wasu iyayen su suke jefa 'Ya'yansu akan hanyar Zina ta dalilin burinsu cewar "SAI TA GAMA DEGREE". Hakanan a bangaren Mazan ma.

Da yawa daga cikin 'Ya'ya Mata akwai wadanda tun shekarunsu basu fi sha biyar ba (15) aduniya, suke da bukatar namiji. Saboda yanayin sinadaran halittar dake jikinsu.

A bangaren Maza ma akwai da dama wadanda tun basu fi shekaru 18 zuwa 20 aduniya ba, zasu ji cewa su aure suke so!.

Kai kanka Uba idan kayi nazari da taka rayuwar zaka iya tuno cewar "TUN KANA 'DAN SHEKARA KAZA ADUNIYA KAKE DA TSANANIN BUKATAR YIN AURE".

Haka kema Uwa idan kikayi nazari zaki fahimci halin da 'Yarki take ciki. Kuma zaki iya kwatanta cewa ayanzu menene tafi bukata arayuwarta!.

Kuma ku iyaye alokacin samartakarku ko 'Yan-Matancinku babu abubuwan dake lalata zukatan yara kamar irin na wannan zamanin da muke ciki. Saboda haka yadda ke kika jure taki sha'awar, ba lallai ne 'Yarki ta iya jurewa ba. Don watakil naki iyayen sun baki tarbiyyar da ta zarce irin wacce kike yiwa taki 'Yar!.

Wasu da yawa sun san abubuwan nan da na lissafo sai dai tsananin Tsoron talauci ne yasa ba zasu amince 'Dansu yayi aure bai yi degree ba..

Suna ganin kamar "IDAN 'YARSU BATAYI DEGREE BA, BA ZATA SAMU MIJI MAI QARFIN ARZIKIN DA ZAI IYA RIKETA BA". Ko kuma idan batayi degree ta samu aikin Office ba, Ba zata samu abinda zata rike kanta agidan Miji ba..

Yarinya ta shekara 25 zuwa Talatin babu Miji babu dalilinsa wai tana karatun Boko.. Tsakani da Allah duk yadda takai wajen Lura da kanta, Ai dole Zuciyarta ta rika kawo mata wasu abubuwa. Dole wani lokacin taji ta samu matsuwar sha'awa. Kuma Kowa yasan cewa Mata sun zarce Maza wajen Matsuwa.

Sannan idan akayi La'akari da irin rayuwar da akeyi a manyan Makarantun gaba da Sakandire, za'a ga cewa ba abu ne mai Wahala ba, Yarinya ta lalace Idan har bata sanya tsoron Allah azuciyarta ba.

Ga Shaidanun Lakcharori, Ga shaidanun Samari, Ga shaidanun Qawaye.. Ga Shaidanun Whatsapp da Facebook, Ga Kuma PRESSURE na tsinanniyar sha'awa wacce Shaitan (L. A) Kullum yake chusa mata azuciya, Babu dare babu rana..

Hakanan a Bangaren Maza, Bisa irin wannan dalilan da na lissafo, Wasu sun afka cikin zina ko Luwa'di, Wasu kuma (Masu Kunya, masu Tsoron Zina) sun shiga yin Istimna'i (MASTURBATION) wanda ke mutukar chutar da lafiyarsu.

Gara namiji komai dadewa zai iya samun aure duk sanda yake so. To amma Mace fa?.

Sai ta gama bokon kuma Maza Su rika tsoron zuwa wajenta koda suna mutukar sonta da aure. Suna ganin kamar ba zata sauraresu ba.. Da haka sai ta jera shekara Uku ko hudu babu wanda yazo hira wajenta!.

Wata kuma sun rika yaudararta kenan. Wannan yazo ya yaudareta ya biya bukatarsa ya tafi, wancan ma yazo yayi ya tafi.. Ta rasa wanda zata kama balle ta tsaida Mijin aure!.

Wata kuma ta Kammale kanta. Ga ilimin ga tarbiyyar, Amma mutane su rika yi mata Mummunan zato : "Ai tunda ta dade batayi auren ban ba, to 'Yar iska ce!" (Wal Iyazu bil Lah).

Ya zama wajibi iyaye su kalli irin wadannan zantukan da idon basira, domin daukar Matakin gyarawa. Ku rika barin 'Ya'yanku suna yin aure tun auren yana sonsu!!.

Kuyi ma 'Yarku aure da zarar ta samu Manemi.. Domin Muhimmancin auren yafi na karatun boko din. Idan ma ya zama dole sai tayi, to tun farko kuyi yarjejeniya tsakaninku da Mijinta cewar zai barta ta Qarasa karatunta. Shikenan.

Hakanan 'danku Namiji : In dai har zaku iya kashe masa Makudan Kudade don yayo Degree ko Masters to mai zai hana kuyi masa auren Ku dauki nauyin rike masa Matar tasa, yaje yayi karatun? Ko kuma ku turasu su tafi tare?.

'Ya'yanku Amanar Allah ce ahannunku. Kuma sai ya tambayeku game dasu. Don haka Ku kiyaye musu :

TARBIYYARSU. 
IMANINSU. 
MUTUNCINSU.

Ku kuma 'Yan uwa 'Yan Boko kuji tsoron Allah ku kiyaye kanku daga afkawa cikin wannan mummunar bala'i wacce ta mamaye Matasa awannan zamani. Ku sani cewa jikinku Amanar Allah ne da ya baku. Kuma akwai ranar da zaku tsaya agabansa, Kowacce ga'ba tayi bayanin abubuwan da kuka aikata da ita.

Ire-iren wadannan batutuwan sune abinda ya kamata Malamai sufi mayar da hankali akai (Wato Gyaran Zukatan Al'ummah da kuma 'dinke 'barakoki acikin al'ummah) ba wai zagi ko gaba ko cin mutuncin juna ba.

Allah yasa mu gyara, Allah shi taimaki Musulunci da Musulmai. Allah shi kiyaye mana yaranmu da Qannenmu da Matanmu da zuriyarmu da dukkan Musulmai baki daya daga sharrin Zina da dangoginta. Ameeeen.

HANYOYIN RABUWA DA MASTURBATION

Hakika matsalar Istimna'i (wato Masturbation) gagarumar matsala ce wacce take shiga zuciyar masu yinta, tayi KAKA-GIDA. Kuma tana da wahalar fita gaba dayanta dole sai dai albarkacin addu'a da kuma yawaita ibada mutum zai samu wadatuwar tsoron Allah azuciyarsa harma ya zamto ba zai iya aikatawa ba.

Mafiya yawan samari suna yi ne bisa niyyar wai zasu kauce ma ZINA. Basu san cewa shima wannan din babban Kaba'ira bane!!

Matasa Maza da Mata da dama sun afka cikin wannan bala'in. Wasu cikin rashin sanin illolinsa, wasu kuma saboda tsabar Fajirci.

Kuma kamar yadda zina take da mutukar Illa tana cutar da lafiyar mutum, ta chutar da hankalinsa, da gurbata tunaninsa, ta cire masa Kwayar Imani da tsoron Allah daga zuciyarsa, to hakanan shima Istimna'i yake lalata rayuwar mutum da mutuncinsa da lafiyarsa.

Lallai wajibi ne ga duk mutumin da yake son kansa da arziki, kuma yake fatan gamuwa da Allah lafiya, ya nisanci Zina da dangoginta irin su Luwadi, Madigo, Istimna'i, da sauransu.

Kamar yadda muka sha fada anan ZAUREN FIQHU, Babbar hanyar da zaka bi/zaki bi domin rabuwa da wannan bala'in sun hada da:

1. Nisantar duk wani hoto ko Video mai nuna tsaraici. (Ka gogeshi daga wayarka)

2. Nisantar shafukan Internet masu nuna tsaraici.

3. Dena abota da fitsararrun abokai / Qawaye.

4. Nisantar duk wajen da ake chudanya tsakanin maza da mata.

5. Ka dena zama kai kadai acikin daki in dai ba ibada kake yi ba.

6. Yawaita karatun Alqur'ani da zikirin Allah. da sauran ayyukan alkhairi.

7. Zama cikin Mutanen kirki, karanta labaran mutanen kirki tare da kokarin koyi dasu.

8. Tuna Allah ako yaushe da kuma tunowa kusancinsa gareka aduk inda kake.

9. Tuna kusancin ajalinka, fitar ruhinka, kwanciyar Qabarinka, Awun hisabinka, da kuma masaukinka na karshe. Wuta ko Aljannah.

10. Fita daga duk wani Group ko shafi na batsa a Facebook ko Whatsapp wanda suke Qunshe da abubuwan batsa, tare da nisantar Friends masu sharing din irin wannan.

Illolin zina da luwadi da madigo (1)...

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin Manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam) tare da alayensa da sahabbansa. Bayan haka, wannan tsokaci ne a kan ma’ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncin kowanensu a karkashin shari’ar Musulunci da Dokta Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo ya rubuto kuma muka ga ya dace a sanya a wannan fili don amfanin jama’a. Ina rokon Allah Ya sa abin ya yi tasiri a kan kowane Musulmi. Bismillah! 
Ma’anar zina da hukuncinta:
Lafazin zina a shari’ance yana nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure, ko an mallake ta a matsayin baiwa ba. Sai dai akan yi amfani da lafazin zina a kan abin da bai kai saduwa ba, kamar yadda ya zo a Hadisin Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ) ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “An rubuta wa dan Adam rabonsa na zina, babu makawa sai ya same shi, zinar idanu ita ce gani, zinar kunnuwa ita ce ji, zinar harshe ita ce magana, zinar hannu ita ce damka, zinar kafa ita ce taku, zuciya kuwa tana kwadayi tana fata, farji kuma shi yake gaskata haka ko ya karyata.” Muslim.
A cikin wannan Hadisi za mu ga yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nuna cewa kowane dan Adam an rubuta masa rabonsa na zina, kuma zai samu wannan rabo babu makawa, sai dai ba za a kama shi da laifi ba, har sai idan ya gaskata abin da idonsa ko kunnensa ko hannunsa ko kafarsa suka jiyar da shi, ta hanyar yin amfani da farjinsa don biyan bukatar wadannan gabbai. Wannan shi ne ma’anar fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a karshen Hadisin, “farji shi yake gaskata haka ko ya karyata.” (Sharhin Sahih Muslim na Imam Nawawi Juz’i na 16, shafi na 216).
Hukuncin zina: 
Zina haramun ce a addinin Musulunci. Allah Madaukakin Sarki Ya haramta ta inda Yake cewa : “Kada ku kusanci zina, domin ita alfasha ce kuma tafarki ne mummuna.” (Isra’i:32).
Malamai suna cewa, fadin Allah “kada ku kusanci zina,” kai matuka ne wajen hana ta, don ya fi a ce “kada ku yi zina.”
Sheikh Abdur-Rahman Assa’idiy yana cewa: “Hani ga a kusanci zina ya fi kai matuka a kan hana yin ta, saboda cewa kada a kusance ta ya hada hana dukkan yin abubuwan da suke gabatar ta kuma suke kawo yin ta, domin kuwa duk wanda ya yi kiwo a gefen shinge, to ko yana daf da fadawa cikinsa, musamman ma a kan irin wannan lamari, wanda da yawa daga cikin zukata suna dauke da abin da yake sawa a afka masa. Sannan Allah Ya siffata zina da cewa alfasha ce. Ma’ana zina wata aba ce da shari’a da hankali suke ganin muninta, saboda keta alfarmar Ubangiji ce da shiga hakkin macen da hakkin danginta da mijinta, kuma bata wa miji shimfidarsa ne da cakuda dangantaka da makamancin haka.” (Tafsirin Assa’idiy).
A wani wurin a cikin Alkur’ani Mai girma, Allah Madaukakin Sarki Ya siffata bayinSa muminai da cewa su ne wadanda ba sa zina, inda Ya ce, “Wadanda ba sa kira ko bauta wa wani tare da Allah; ba sa kashe rai da Allah Ya haramta sai da hakki; kuma ba sa zina, duk wanda ya aikata haka zai gamu da azaba.” (Alfurkan: 78). 
Ya tabbata a cikin Hadisi an tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) a kan wane zunubi ne ya fi girma, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Shirka da Allah alhali Shi ne Ya halicce ka.” Sai aka ce, ‘sai wanne?’ Sai ya ce, “Sannan kashe danka don kada ya ci tare da kai.” Sai aka ce, ‘Sannan sai wanne?’ Sai ya ce, “Ka yi zina da matar makwabcinka.” (Buhari). 
Allah Madaukakin Sarki Ya sanya hukuncin wanda duk ya yi zina kuma ya taba aure, a jefe shi, namiji ko mace; idan kuwa bai taba aure ba, sai a yi masa bulala dari, sannan a bakuntar da shi a wani gari daban tsawon shekara guda (ma’ana a daure shi a kurkuku).
Duk wanda ya kalli hukuncin zina, zai ga Allah Ya kebance shi da wasu abubuwa masu yawa, saboda munin zina. Ga kadan daga cikin abubuwan da hukuncin ya kunsa:
• Kausasawa wajen ukubar mazinaci, ta hanyar jefewa. Ko kuma bulala da bakuntarwa shekara guda.
• Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya yayin da ake musu ukuba. Allah Ya ce: “Mazinaciya da mazinaci ku yi wa kowane daya daga cikinsu bulala dari. Kada ku ji tausayinsu a cikin addinin Allah, in dai kun yi imani da Allah da Ranar karshe.” (Annur:2). 
• Yi musu ukuba a gaban mutane. Ba a yarda a yi musu a boye ba. Allah Ya ce: “Wasu bangare na muminai su halarci wajen yi musu ukuba (haddi).” (Annur:2).
Duk wadannan abubuwa suna nuna mana munin zina da rashin kyanta a Musulunci. Imam Buhari ya kawo a cikin ingantaccen littafinsa daga Maimun Al’audiy ya ce, “A lokacin Jahiliyya na taba ganin wani biri da ya yi zina da wata biranya, sai sauran biran suka taru suka jefe su.”
Mafi munin zina ita ce wadda mutum zai yi da mahaifiyarsa; sai da muharramarsa; sai wadda zai yi da mata (ko ’yar) makwabcinsa. Allah Ya kare mu.
Illolin zina: 
Babu ko shakka duk mai hankali ya san cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, wadanda suke shafar mazinacin ko mazinaciyar, ko su shafi al’umma gaba daya. Ga wasu daga cikin illolinta:

1. Zubar da mutunci da jawo wa kai kaskanci: Duk matar da ta yi zina, to ta jawo wa kanta da danginta da mijinta kaskanci, ta kuma zubar musu da mutunci a idon duniya. Idan har ta samu ciki ta haihu, sannan ta kashe dan, to ta hada laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai. In kuma ta bar shi, to kuma ta shigar wa mijinta ko danginta, wanda ba ya cikinsu. Idan kuwa mai zinar namiji ne, to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da tabewa, wanda hakan lalata duniya ne gaba daya.

2. Zina ta hada dukkan sharri gaba daya: Saboda a cikin zina akwai rashin tsoron Allah; rashin kunya; rashin tsantseni; rashin cika alkawari; karya da butulci da sauransu. Duk kuwa wadannan munanan halaye ne a Musulunci.

3. Zina tana haifar da cututtuka da mutuwar zuciya da sanya zuciya ta zama bakik-kirin da samun kai cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali da nutsuwa a koyaushe. Bincike ya tabbatar da cewa cutar kanjamau ta fi yaduwa ta hanyar zina fiye da kowace hanya da ake iya daukar cutar daga gare ta, sannan ta hanyar cutar akan kamu da miyagun cututtuka masu mugun hadari. 

4. Zina tana haifar da talauci da musiba a bayan kasa, saboda da duk namijin da yake mazinaci, to ba ya iya tattali, kullum kudinsa suna wajen matan banza, duk abin da zai samu, ba zai amfanu da shi ba yadda ya dace, a banza zai tafi. Haka nan duk matar da take mazinaciya ce, duk abin da ta samu yana karewa ne wajen yadda za ta janyo hankalin maza zuwa gare ta, Allah kuma Zai zare wa dukiyarta albarka.

Ma’ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu .....

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai.  Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa.  
Bayan haka, mun kwana a karshen illa ta 5 daga cikin illolin luwadi, yau ga ci gaba daga illa ta:

6.    Luwadi yana haifar da munanan cututtuka, irin su rashin rike bayan gida, kuraje, sanya zuciya ta yi baki wuluk, bacewar basira da kyakkyawan tunani, rashin kunya da sauransu.

7.    Luwadi yana kawo kaskanci da wulakanci da tozarta, a duniya da Lahira.

8.    Saduwa da mace ta dubura mummunan abu ne, wanda Ibnul kayyim - Allah Ya yi masa rahama - yake cewa, “Ba a taba halatta saduwa da mace ta dubura a harshen wani Annabi da Allah Ya aiko ba.” 

9.    Mai luwadi bai kai darajar dabbobi ba, saboda dabba ma ba ta haka.

10.     Mai luwadi - in bai tuba ba - ba ya rabuwa da duniya lafiya, ko dai Allah Ya tozarta shi, kowa ya san aikinsa, ya wayi gari ba ya da mutunci a idon duniya gaba daya, ko kuma Allah Ya jefa masa wata mummunar cuta da zai rika fatan ya mutu kowa ya huta, saboda muninta. Allah Ya kiyashe mu.

Madigo da hukuncinsa:

Madigo shi ne mace ta biya bukatarta da mace, ta hanyar rungumar juna da hada gaba da sauransu.
Madigo haramun ne a addinin Musulunci. Malamai sun sanya shi daga cikin manya-manyan zunubai. Sai dai shari’a ba ta ayyana wani hukunci zaunanne da za a yi wa masu madigo ba. Alkali ne zai duba me ya dace ya yi musu na hukunci, bulala ko dauri ko kora ko tozartawa, ko kuma a hada musu duka. Duk dai hukuncin da alkali ya yanke na razanarwa da tsoratarwa ya yi.  (Duba Almausu’atul Fikihiyyatul Kuwaitiyya da Almugniy na Ibnu kudama).

Illolin madigo:
Madigo, kamar sauran abubuwan da suka gabata ne (yana da illa) wajen haifar da cututtuka da bala’i da musiba ga mai yin sa. Ga kadan daga cikinsu:

1.    Madigo fita ne daga dabi’ar da Allah Ya halicci mace a kanta, ta jin dadi da da namiji ba mace ’yar uwarta ba.

2.    Cikin Madigo akwai rashin kunya da fitsara, alhali Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: “Kunya alheri ce gaba dayanta.” A wata riwaya: “Kunya ba ta kawo komai sai alheri.” Buhari ne ya rawaito.

3.    Madigo yakan haifar da cutukan zamani. A wani bincike da aka gabatar, ya tabbatar da za iya daukar cutar kanjamau ta hanyar madigo, idan aka yi da wadda take dauke da ita, kamar yadda za a iya samun ciki ta hanyar madigo, idan mace ta yi da wadda ba ta dade da saduwa da da namiji ba. Haka nan likitoci sun tabbatar da madigo yana iya jawo rashin haihuwa.

4.    Ana iya rasa budurci ta hanyar madigo, wanda hakan ba karamin tozarta ba ne ga budurwa ta rasa budurcinta kafin ta yi aure.

5.    Mai madigo takan rayu cikin kuncin zuciya da kunarta, saboda Allah zai debe mata natsuwa a tare da ita, Ya maye gurbinta da kunci da damuwa. Wata budurwa ’yar shekara ashirin tana ba da labarin irin yadda ta samu kanta cikin damuwa da bala’i bayan rabuwarta da abokiyar madigonta. Tana cewa: “Na kasance budurwa ’yar shekara ashirin, ina son wata kawata sosai tsawon wasu shekaru masu yawa, har dai muka fara madigo a tsakaninmu, ta shiga raina matuka, na zama duk abin da take so shi nake yi, har ma ya zamana wani lokaci ana samun sabani tsakanina da ita idan na ga wani ko wata suna kaunarta, saboda yadda nake kishinta. Wata rana sai wannan kawar tawa ta yi aure, abubuwa suka canza, ta ce dole ne mu rabu. Haka muka rabu, ni kuma na shiga wani hali na jin zafi da radadi a jikina da zuciyata! Ciwon kai, ciwon idanu, ciwon jiki, na je wajen likitoci amma ban samu wata waraka ba, wayyo! Ni yanzu yaya zan yi, ga shi na tuba, amma fa ina so in koma wajenta, yaya zan yi!? Wannan kadan ke nan daga illar madigo.

6.    Madigo yakan hana ’ya mace zaman aure, domin duk wadda ta saba da shi, to zai yi wahala ta rabu da shi, wanda wannan zai sa ta kasa wadatuwa da mijinta, sai ta rika fita tana yi, har idan Allah Ya tona asirinta, mijinta ya sake ta, saki na wulakanci, ko kuma ta nemi saki da kanta ta je ta ci gaba da madigonta, don haka: “Maganin yaya za a yi, (shi ne) kada a fara.”

7.    Mai madigo ba ta karewa da duniya lafiya, ko dai tozarta a duniya, ko kuma haduwa da mummunar cuta da bala’in da ba a warkewa, sai dai kabari!

8.    Madigo dabbanci ne! Kai! Dabba ma ta fi ’yar madigo.

9.    Cikin madigo akwai cin amanar Allah Mahalicci, saboda an aikata abin da Ya hana, haka kuma akwai cin amanar iyaye ko miji.

10.    Haduwa da azabar Allah a Lahira, idan ba a tuba ba.
Wannan kadan ke nan daga cikin illolin da madigo yake haifar wa masu yin sa. Allah Madaukakin Sarki Ya kare mu.

Ma’ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu.....

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, sallallahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa. 
Bayan haka, mun karanci bayanai kan ma’ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu, to yau ga ci gaba daga manuniya ne kan:

Hanyoyin Kare Kai Daga Zina Da Luwadi Da MadigoSaboda hikimar Ubangiji da rahamarSa, duk abin da Ya haramta wa bayi, to za a bude wata kofar da mutum zai biya bukatarsa ba tare da ya afka wa wancan abin da Allah Ya hana din ba. Wannan abu haka yake a nan ma, domin dai mun ji irin tarin illolin da suke tattare da yin zina da luwadi da madigo, to amma babu yadda namiji ko mace za su rayu ba tare da sun sami inda za su zubar da sha’awarsu idan ta taso ba, saboda haka sai Musulunci ya halatta wadannan abubuwa masu zuwa don kauce wa afkawa cikin zina:

1. AURE: Allah Madaukakin Sarki Ya halatta wa maza su auri mata, inda yake cewa: “To ku auri abin da kuke so na mata, bibbiyu (ko) uku-uku (ko) hurhudu. Idan kuwa kuna tsoron ba za ku iya adalci ba, to ku auri daya, ko kuma abin da damarku ta mallaka. Wannan shi ne abin da zai sa ba za ku karkace ba.” (Annisa’i: 3).
Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) kuma yana cewa, “Ya ku taron samari, duk wanda ya sami iko (ma’ana zai iya rike mata) to ya yi aure, domin shi ne mafi abin da yake sa runtse ido, kuma mafi sawa a tsare farji. Duk kuwa wanda bai samu iko ba, to ya yi azumi, domin (shi azumi) kariya ne a gare shi.” Bukhari da Muslim.
Wannan aya da hadisi suna nuna mana halaccin mutum ya yi aure, kuma ya auri matar da yake so, wadda ta kwanta masa a rai, matukar ba ta cikin wadanda Allah Ya haramta masa ya aura. Saboda haka da mazinata da ’yan luwadi da masu madigo za su yi tunani da sun ga yadda Musulunci ya sauwake musu hanya, ta hanyar su yi aure, sai ya zama duk abin da za su yi halal ne, in ma sun yi niyya Allah Ya ba su lada, kamar yadda hadisi ya nuna.

2. Mallakar bayi: Musulunci ya halatta wa namijin da ya mallaki baiwa ya yi sadaka da ita, don kare mutuncinsa da mutuncinta. Ko kuma ya ‘yanta ta ya aure ta.

3. Azumi: Yin azumi, kamar yadda hadisin da ya gabata ya nuna [wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito] kariya ne a gare shi, saboda (shi) mai azumi, an umarce shi da ya kare gabbansa daga barin haramun, kada ya yi aikin banza, ko maganar banza, ko kallon banza, wanda kuwa duk zai yi azumi ya kiyaye gabbansa daga wadannan abubuwa, to babu ko shakka Allah zai ba shi tabbata a kan da’arsa, ba zai kyale shi ga shaidan ba, har ya kai shi zuwa ga (aikata) haramun.

4. Nisantar Abubuwan da Suke Motsa Sha’awa: Ya zama mutum yana nisantar duk wani abin da zai motsa masa sha’awarsa har ya kai shi zuwa ga neman mata, ko luwadi, ko madigo, kamar kalle-kallen finafinan batsa, karanta mujallun banza, raye-raye tsakanin maza da mata, sauraron kide-kide da sauransu. Haka nan da nisantar wuraren da ake saba wa Allah, inda yake hada maza da mata, ana shedana da ayyukan banza.

5. Shagalta da ayyukan alheri: Duk wanda zai shagaltar da kansa (wajen gudanar) da ayyukan ibada da alheri, to ba zai sami lokacin da zai je zuwa ga zina ko luwadi ko madigo ba. Musulmi na hakika, ba shi da wani lokaci da zai tafiyar da shi wajen saba wa Allah, duk lokutansa na ibada ne da tsoron Allah.

6. Tsoron Allah a koyaushe: Kamar yadda Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Ka ji tsoron Allah a duk inda kake”. 
kofar Tuba A Bude Take
Wani ko wata za iya tunanin cewa yanzu na ji wa’azi, to yaya zan yi in tuba in daina, kuma shin ma Allah zai karbi tuban nawa, bayan dukkan wadannan abubuwa da na aikata? Sai mu ce:
Babu wani zunubi a bayan kasa da Allah ba Ya gafarta shi, matukar dai mai yin sa ya tuba, tuba ingantacciya, saboda Allah Yana cewa, “Ka ce, ya ku bayiNa wadanda suka yi wa kansu barna kada ku debe kauna ga rahamar Allah, hakika Allah Yana gafarta zunubai gaba daya, lallai shi Allah, Mai gafara ne, Mai jinkai”. (Surar Azzumar, aya ta 53). Sannan Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Allah Ya sanya wata kofa a wajen mafadar rana, fadinta tafiyar shekara saba’in ce, saboda tuba, ba kuma za a rufe wannan kofar ba, matukar dai rana ba ta bullo daga inda kofar take ba”. Tirmizi ne ya rawaito wannan hadisi.

A wannan aya da hadisi, za mu ga yadda Allah Madaukakin Sarki, saboda rahamarSa da falalarSa, Ya bude tangamemiyar kofar karbar tuba, har zuwa lokacin tashin alkiyama. Don haka babu wani zunubi da mutum zai yi a fadin duniyar nan, face in ya tuba, Allah zai karbi tubansa. Abin da dai ya wajaba a kiyaye yayin tuban shi ne:

• Yin nadama a kan abin da ya gabata, ya zama yana tunawa kuma yana damuwa, yana nadama, yana jin yaya ma aka yi ya aikata wannan laifin!

• kudurcewa a zuciya yayin tuba, cewa ba zai kara koma wa wannan laifi ba, har karshen rayuwarsa.

• Barin wannan sabon, in yana cikin yi ne yayin da zai tuba, kada ya ce bari in karasa, sannan sai in tuba.

• Yin tuban a lokacin da Allah Yake karba, shi ne kafin tashin alkiyama, kuma ba lokacin da yake gargarar mutuwa ba. Hakika Allah ba Ya karbar tuba a wadannan lokatai guda biyu, kamar yadda Alkur’ani da hadisi suka nuna.

• Ya zama ya sauke nauyin wani da ya hau kansa, idan kudi ne ya biya shi, in cin mutunci ne ya nemi ya yafe masa.
Wadannan su ne abubuwan da mai tuba zai kiyaye da su yayin tubarsa. Allah Madaukakin Sarki Ya sa mu dace.
Ina So In Tuba Sai Dai…
Da yawa daga cikin mutane suna son su tuba su bar zunubin da suke yi, sai wasu abubuwa sukan zo su sha gabansu, su kange su ga barin tuba din, har kuma su halaka suna kan wannan sabon, to amma mutum musulmi, wanda ya san abin da yake, ya san babu wani Dattin Zina

Zina wata irin dau'da ce wacce idan ta kama zuciyar 'dan Adam tana da wuyar wankuwa.. Kuma ko da ta wanku, batta wankuwa gada daya sai kaga gurbinta yana nan.

Duk zuciyar da ta riga ta chudanya da Zina, ta zama zuciya mai Ha'inci. Kuma ma'abocinta ba zai ta'ba zama cikakken mumini ba. Sai dai idan ya tuba.

Bincike ya nuna cewa NAMIJI idan yayi nisa acikin Zina, har zuciyarsa takan kawo masa sha'awar yi da muharramansa ma. Kamar Uwarsa wacce ta haifeshi, ko dangin Uwarsa, ko dangin Ubansa, ko Qannensa mata... Wani lokacin zuciyarsa takan jefa masa sha'awarsu.

Hakanan Mace idan ta zama Mazinaciya, babu wani Minti guda acikin rayuwarta fache ta tanadeshi ne domin aikata zina ko kuma aikat duk abinda zai ja hankalin mazinata 'yan uwanta.

Zina mugun ciwo ne wanda yakan kashe mutum ta ciki, tun kafin ya kasheshi ta waje.

Wannan yasa Manzon Allah (saww) yace "MAI ZINA BA MUMINI BANE SHI, YAYIN DA YAKE ZINA".

Awani hadisin kuma ya lissafta TSOHON MAZINACI acikin mutanen da ba zasu shiga Aljannah ba.

Zina idan tayi nisa azuciyar mutum, takan lalata mafiya yawan zuriyarsa.... Koda bayan ransa sai. Kaga ana samun yawaitar masu koyi dashi acikin zuriyarsa.

'Yan Uwa. Mu nisanci ZINA kuma mu nisanci duk masu yinta... Domin ita dabi'a takan yi naso ne.

YAYI ZINA DA MATAR AURE!!

Assalmu alikum malam. Don Allah a sakaya sunana. Malam don Allah ayi kokari duk abinda na fada a wallafa shi a wannan zauren mai albarka don ya zama darasi garemu baki daya.

Ni dai ma'aikacine kuma yanzu haka ina wata jiha don aiki kamar yadda daga lokaci zuwa lokaci aiki yakan kaini. Zuwata wannan jihar sai na hadu da wani abokina har ya zamanto banda wurin fira sai wurinshi.

A nan wata rana na hadu da wata yarinya inda daga karshe dai na karbi lambar wayarta. Hira tsakanina da yarinyar nan ya wuce na tsakani da Allah daga karshe har sai da muka yi zina (Astagrirullah wa atubu ilaihi).
Kafin wannan mummunan abin ya faru, abinda na iya sani a game da yarinyar daga wurin abokina shine; ta taba aure amma mijin ya gudu ya barta ba a san inda yake ba, kusan shekara daya kenan amma yanzu kotu ta raba auren wand ita ko da wasa bata taba fada min hakan ba. Sai dai cewa tayi tana da saurayi amma ya yaudareta ya gudu ya barta.

Mun ci gaba da abinda dani da ita muka kira soyaiya duk da cewa wallahi har cikin zuciyata ni na san bana sonta sai dai ban san abinda ke cikin nata zuciyar ba.

Kada dai in tsawaita wannan labarin, daga karshe dai ranar wannan sallan babba sai ita da kawarta suka kawo mini abinci sai naji a zuciyata kuma yanzu babu wanda hankalina ya karkata wurinta sai kawar. A dai dai wannan lokacine ita yarinyar take cemin zata yi tafiya zuwa wani wuri amma ba zata dawo ba sai bayan wata daya.

Bayan ta tafi sai na koma kiran ita kawar a waya wanda daga baya na samu hadin kanta da sunan soyaiya. Cikin irin firar da mukeyi ne, ita kuma don ta samu gindin zama sosai a zuciyata ta fada min abinda shine dalilin tashin hankalin da bana taba shiga ba. Watau abinda ta fada min shine. Ko na san cewa wannan yarinyar tana da aure? Nace wallahi ban sani ba. Kuma hakane wallahi ban sani din ba. Abinda na sani shine an kashe aurenta da mijinta da ba a san inda yake ba.

Tafiyar nan da take cewa tayi zatayi wata daya a wurin ashe gidan mijinta ta koma. Kuma duk da cewa ta koma gidan mijin tana kirana kuma muna waya har da maganganu na batsa. Amma ban san cewa a gidan mijin take ba.
Allah ya gafarta malam. A daidai wannan lokacine nake baran addu'a a wurin yan uwa, ubangiji Allah ya yafemin wannan abinda na aikata. Lallai wannan ya zama dalilin tuba a gareni. Kuma ina mai tuba zuwa ga Allah. Ina son wannan abin ya zamo darasi ga kowa. Maza da mata, muji tsoron Allah.

Shin ko Allah zai karbi tubata? Sannan kuma malam wadanne irin addu'o'I ya kamata in rika karanta wa don tuba da neman yardar Allah. Ina cikin tashin hankali wanda ban taba shiga cikinsa ba a rayuwata.

Allah kadai yasan halin da nake ciki har a yanzu da nake wannan rubutun.
(Al'ameen)

AMSA
******
Tabbas kayi katobara, ka zalunci kanka. Ka aiwatar da Babban Kaba'ira.

Amma babban abinda ya bani haushi kuma ya bani mamaki acikin wannan dogon labarin naka shine:
Wato kai ba wai kana yin nadamar aikata Zina bane. A'A. Kai kana yin nadama ne kawai saboda ance maka matar aure ce!!!

Agaskia dunia ta rudeka. Kuma shaitan ya riga ya rinjayeka. Ka zama nasa.

Kuma tabbas mazinata suna haduwa da Qaskanci da wulakanci da Qaskanci da talauci tun daga nan dunia kafin aje lahira.

Don haka ka tuba izuwa ga Allah. ka kaurace ma zinan da kakeyi. Kuma ka dena duk wata hulda tare da abokananka wadanda kuke yin zinar nan tare..

Ka yawaita istighfari da aiyukan alkhairi wadanda Allah yake kankare Zunuban bayinsa dominsu. (Kamarsu azumin nafila, tasbihi da salatin Annabi saww.)

Sannan kaje ka nemi gafarar mijinta domin shiga hakkinsa da kayi. Idan kuma neman yafewarsa zata janyo maka tozarta da kuma tashin hankali, to sai kaci gaba da yi masa addu'a. Kana nema masa gafara awajen Allah.

​ZINA DA KANIN MIJI (SUBHANALLAH) 

ASLM  Mallam na samu matsala ne a rayuwata   ina zaune da mijina shekaranmu 7 da aure akwai kaninsa da yake bibiyata malam tun bana kulashi har ya kai yenzu har yakai muna wasa dashi.

Nayi nayi ya bari yaki bari. mai ya kamata inyi?

Har ya saba inya shigo ya danneni har sai ya biya bukatansa akaina kuma bana iya che masa komai. Malam ataimaka mun da addu’oi da shawarwari.
AMSA

*******

Wa alaikis salam. 

Hakika kin aikata kuskure babba. Domin kuwa bayan shirka babu wani zunubi mafi girma awajen Allah kamar zina. 

Manzon Allah (saww) yace : “MAZINATA ANA HURA MUSU WUTA NE BISA FUSKOKINSU (RANAR ALKIYAMAH KENAN). 

(Imam Tabaraniy ne ya ruwaito). 
Sannan acikin hadisai da dama Manzon Allah (saww) ya bayyana cewar Akwai wani ruwa mai bala’in doyi wanda ke fita ta farjojin Mazinata acikin Wuta. Wannan ruwan dashi ake yiwa sauran ‘yan Wuta Azaba. 

Sannan acikin wani Sahihin hadisi wanda Imamul Mundhiriy ya ruwaito acikin Targheeb wat-Tarheeb, Manzon Allah (saww) yace: “ALLAH YANA KUSANTOWA GA BAYINSA, SAI YAYI GAFARA GA DUK MAI NEMAN GAFARA. AMMA BANDA MATAR DAKE ZINA DA FARJINTA…. “.

Ya zama wajibi kiji tsoron Allah ki dena domin kuwa wannan laifin zai iya janyo miki bala’i da tozarta da wulakanta dake da danginki da iyayenki tun daga nan duniya. Aranar lahira kuma Farjin naki da kike zinar dashi, da kuma sauran gabobin jikinki sune zasu tona asirinki agaban Zatin Allah, ga dukkan halittu suna kallonki. 

Zata yiwu ki samu ciki ta dalilin wannan Zinar, kuma ki shigo ma mijinki da wannan cikin (Ma’ana ba zai gane cewa cikin ba nasa bane). Alhali Manzon Allah (saww) yace:

“DUK MATAR DA TA SHIGO MA WASU MUTANE DA WANI WANDA BA CIKINSU YAKE BA, TO ITA BA KOMAI BACE AWAJEN ALLAH. KUMA (ALLAH) BA ZAI SHIGAR DA ITA ALJANNARSA BA… “

(Nisa’iy hadisi na 3481, Abu Dawud Hadisi na 2263).

Shi kuwa wannan Qanin Mijin naki yaci amanar Allah da Manzonsa (saww), Kuma yaci amanar ‘Dan uwansa (wato mijinki). Kuma yana daga cikin mutanen da Allah yake yin tsinuwa agaresu. 

Manzon Allah (saww) ya gaya ma Sahabbansa cewa “WALLAHI MUTUM YAYI ZINA DA MATAYE GUDA GOMA, SHI YAFI SAUKI AGARESHI (WATO SAUKIN AZABA AKANSA) FIYE DA YAYI ZINA DA MATAR MAKOBCINSA”.

(Imamu Ahmad da Tabaraniy ne suka ruwaitoshi). 

Acikin riwayar Ibnu Abid dunya kuma daga Sayyiduna Abdullahi ‘dan Umar (ra) : “WANDA YAYI ZINA DA HALAL DIN MAKOBCINSA (WATO MATAR MAKOBCIN KO KUYANGARSA) ALLAH BA ZAI DUBESHI BA ARANAR ALQIYAMAH (WATO BA ZAI MASA KALLON RAHAMA BA) KUMA BA ZAI TSARKAKESHI BA. KUMA ZAI CE MASA “SHIGA WUTA TARE DA MASU SHIGARTA)”.

To in dai haka lamarin yake akan matar Makobci, to yaya kuma matar ‘Dan uwa?? 

Saboda guje ma faruwar irin wannan Fasadin shi yasa Manzon Allah (saww) yace : “KADA WANI MUTUM YA KEBANCE TARE DA WATA MACE, FACHE SAI TARE DA MUHARRAMINTA”.

Sai wani yace “Ya Rasulallahi shin Makusancin Miji fa?”. 

Sai Manzo (saww) yace “MAKUSANCI AI SHINE MUTUWA” (Wato shine yafi ‘barna kenan). 
Abinda zakiyi shine :

– Da farko ki tuba zuwa ga Allah ki janye jiki daga wannan kwarton fasikin dake zuwa miki. 

– Ki hanashi shigowa amma idan bai hanu ba, Ki sanar ma mijinki cewa lallai ya hana wannan Qanin nasa shigowa inda kike. 

– Ki rika tuna lahirarki da kuma tsayuwarki agaban zatin Allah. Da kuma kusancin Allah gareki ako yaushe. 

– Ki sani cewa Biyan bukatar Sha’awar Minti biyar zata iya janyo miki Wulakantar duniya da lahira. 

– Ki tuna rayuwar yaranki da kuma tarbiyyarsu. Kuma ki dubi amanar Mijinki da kike ci. 

Ki Yawaita Istighfari da Azumin nafilah domin samun tsarkaka daga wannan alfashar. 

– Idan Mijinki ba mazauni bane, gara ki matsa ki bishi wajen da yake aiki ku zauna achan domin samun tsira da Imaninki da mutuncinki. 

– Ki rika yin wannan addu’ar domin nisanta kanki daga alfasha : “ALLAHUMMA JANNIBNEE MUNKARATIL AKHLAQI WAL AF’ALI WAL AHWA’I”.

Allah ya sawwake ya gafarta miki ya shiryeki tlya tsamoki daga kowanne laifi, tare damu baki daya. 

WALLAHU A’ALAM. 

HANYOYI 14 DA ZAKA BI DOMIN GUJEWA AIKATA ZINA:

Babban Maganin da zai hanaka yin Zina, shine:

1. Tsayuwa abisa tafarkin Allah da Manzonsa (saww) da gaskiya.

2. Cikakken jin tsoron Allah afili da boye. 

3. Kulawa da yin Sallah akan lokaci, kuma acikin Jam’I. Tare da neman ilimin sanin Sallar.

4. Zikirin Allah safe da yamma tare da neman tsarinsa daga Sharrin Shaitan ako yaushe.

5. Tuna girman Allah da kuma Kusancinsa gareka/gareki.

Yana tare dakai/dake alokacin da kuke aikata wannan Kaba’irar

 6.Tunowa da girman azabar da Allah ya tanadar ma MAZINATA alahira.

7. Tunowa shaitan da kuma kaidinsa da yake Qullawa domin hallakar da ‘Yan Adam.

8. Gujewa kadaituwa da duk wata Matar da ba Muharramarka ba/ko Namijin da ba Muharraminki ba.
9. Kaucewa kalle-kallen fina-finan batsa. Ko kuma wakoki da hotunan batsa.

10. Kaucewa abota ko Qawance da duk wani saurayi Mazinaci ko budurwa Mazinaciya.

11. Ka tuna cewar Wannan da zaka yi zinar da ita: 

‘diyar wani ce, Qanwar wani ce, Yayar wani ce.

Watarana kuma zata zama Uwar wani.
To yadda kayi Zina da ita, kaima sai anyi Zina da Uwarka, ko Qanwarka, ko yayarka, ko ‘yar da ka haifa.

12. Addu’ar neman tsari daga Miyagun ayyuka, da mummunan tunani.

“Allahumma inni a’uzu bika min Munkaratil Akhlaaqi wal Af’aali wal Ahwa’I.”

13. Daga karshe kuma ka tuna cewa zaka iya kamuwa da wata mummunar chutar da zata zamanto ajalinka.. Kuma koda baka kamu da Chutar zahiri ba, Wallahi in dai ka aikata zina sai chutar Munafurci ko Fasikanci ta shiga zuciyarka. 

14. Tuno ranar da za’a tsayar da kai agaban Allah, a ranar taron Alqiyamah.. Ga iyayenka da Kakanninka har Jikokinka da jikokin-Jikokinka.. agabansu al’aurarka zata bada shaidar cewa Ka aikata abu kaza da ita arana kaza, awaje Kaza.. Mala’iku kuma zasu kawoshi arubuce. 

Fatanmu shine Allah shi kiyayemu baki daya daga wannan mummunan aiki. Wadanda kuma shaitan ya riga ya rudesu, to Allah yasa wannan rubutun ya zama dalilin tubansu. 

KU KIYAYI ZINA

A’amash ya ruwaito daga Sufyan daga Huzaifah bn Alyaman (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:

“YA KU JAMA’AR MUSULMAI, INA GARGADINKU AKAN ZINA (KU NISANCETA). DOMIN ACIKINTA AKWAI ABUBUWA GUDA SHIDA :

GUDA UKU ADUNIYA, GIDA UKU KUMA A LAHIRA. AMMA WADANDA SUKE ANAN DUNIYA SUNE :

1. Gushewar Kwarjini. 

2. Dawwamammen Talauci. 

3. Gajartar rayuwa (Wato rayuwarsu ba zatayi tsawo ba). 
AMMA WADANDA ZASU RISKA A LAHIRA SUNE :

1. Fushin Allah. 

2. Mummunan Hisabi. 

3. Dawwama acikin Wuta. 

A duba littafi mai suna “Akhbarun Nisa’,  babin dake magana akan haramcin zina. 

Ya Allah ka kiyayemu daga aikata zina da dangoginta. Ka tsare mana Qannenmu da ‘ya’yanmu da Matanmu daga sharrin Zina da Mazinata. 

YA’DUWAR ZINA ACIKIN AL’UMMA

Acikin kashi na farko munyi magana akan illolin da ya’duwar zina take kawo ma al’ummah. Yanzu kuma in sha Allahu zamu duba muga wasu daga cikin dalilan da suka kawo wannan bala’i :

1. TALLE : Mafiya yawan yara Matan dake yawon talle acikin kasuwanni, Garejoji, Tashoshin Mota, da Unguwanni, suna cikin hatsarin afkawa cikin wannan mummunar dabi’a. Ba don komai ba sai saboda yadda kullum zasu rika jin kalamai na batsa da Kuma Miyagun wasanni irin na batsa da suke samu daga Shashashun samari da kuma tsofaffin ‘Yan tasha. 

2. WAYOYIN SALULA : Wayoyin Salula suna taka mummunar rawa cikin yaduwar fasadi da lalacewar tarbiyyar al’ummah. Musamman ta bangaren Hotuna da Bidiyo na batsa da recording na kalmomin batsa wanda Matasa maza da Mata suke turawa a wayoyinsu. 
Yara Qanana sukan kalli Hotunan yadda ake jima’i. Daga nan kuma sai Shedanci ya shiga zukatansu su fara tunanin hanyoyin da zasu bi su rika samun biyan bukatarsu,  alhali da chan irin wannan tunanin bai ta’ba shiga kwakwalwarsu ba. 

3. WHATSAPP : Ita ma kafar sadarwa ta whatsapp tana taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar al’ummah. Harma ta zarce Facebook ko Twitter. 
Domin kuwa a Whatsapp ne watsatsun Samari da ‘Yan Mata (har ma da wasu Matan auren) suke bude groups musamman don koyar da zina!!.
Ta wannan hanyar suke sabawa da juna har su rika haduwa da juna. Akwai ma Kungiyoyin Matan aure ‘Yan Madigo wadanda har auren juna suke yi. (Wal Iyazu bil Lahi). 

4. MAKARANTUN SAKANDIRE : Akwai Yara Mata da dama wadanda sun lalace ne tun a Makarantun Sakandiren kwana (Boarding Schools) ta sanadiyyar Malamansu dake tursasa musu suyi Zina dasu, Ko kuma su atsakanin Junansu su rika aikata madigo. 
Hakanan a bangaren Mazan ma wasu tun daga Sakandire suke zama ‘Yan Luwa’di ta hanyar yi da junansu ko da Malumansu. 

5. MANYAN MAKARANTU : Su ma wadannan sun zama manyan dalilan watsewa ga wasu ta dalilin chakuduwar jinsi (Maza da Mata awaje guda). 
Zaka ga har abota ake Qullawa atsakanin Mata da Maza. Sai kaga Matar aure ko Qatuwar Budurwa ta Qulla abota tsakaninta da wani Qato haka kawai saboda ajinsu guda. 
Hakanan munsha jin yadda wasu lalatattun lakcharori suke tursasa yara Mata wajen yin zina dasu saboda su basu Maki (Marks). 

6. FINAFINAI : Ya’duwar Fina-finai na waje da kuma na gida shima ya taimaka wajen watsewar al’amura. Ba don komai ba, idan ka lura da yadda rayuwar Matan hausawa take acikin shekarun 1980 zuwa 2000 Zaka ga ba daidai take da wacce mukeyi yanzu ba. 

Tun daga salon Dinkunan da suke sanyawa, da kuma yadda suke kula da tarbiyyar yaransu, da kuma biyayyarsu ga Mazajen aurensu. 

7. WURAREN PARTY : Idan akayi la’akari da yadda kullum harkokin Party suke Qara bunkasa atsakanin Matasa da kuma irin watsewar da akeyi awajen, lallai za’a fahimci cewar Harkar Party tana daga Miyagun abubuwan dake addabar tarbiyyar al’ummah.
Ana haduwa Maza da Mata awajen kuma ana aikata haramtattun abubuwa iri-iri wadanda ba sai na lissafa ba. 

8. HIRAR ZAMANI : Hira irin ta Samari da ‘Yan matan Zamani itama babbar jigo ce wajen yaduwar Zina. irin wannan hirar ta bambanta da wacce akeyi a shekarun baya – 
– Kadaicewa da juna (Haramun ne). 

– Ta’ba jikin Juna (Haramun ne). 

– Zuwa Dakin Samari (Haramun ne).

– Hirar Batsa. (Haramun ce). 
To wannan ka’dan kenan daga abubuwan dake faruwa a sakmakon hirar nan irin ta Matasan zamani. 

9. MIYAGUN SUTURA : Miyagun suturar da Matan zamanin nan ke sanyawa wanda ke bayyanar da siffar jikinsu, ita ma babbar musibah ce wacce ta Qara habbaka ya’duwar zinace-zinace. Ba don komai ba, sai yadda hakan ke Qara janyo hankulan Wasu Mazajen da kuma Motsa Haramtacciyar sha’awa a zukatansu. 
A Kauyuka abin da sauki-sauki. Amma a birane zaka ga har Matayen aure masu manyan Yara ba’a barsu a baya ba. (Allah shi kiyaye). 
Ya Allah albarkacin wannan Wata na Ramadhana da Alqur’aninka wanda ka saukar acikin watan, da kuma wanda ka girmamashi da Alqur’ani, Ka yaye mana wadannan matsalolin, Ka tsarkake zukatanmu ka tsaftacemu daga dukkan alfasha don falalarka da rahamarka. Ameeen. 

 nayi bayanin wasu manyan dalilan dake janyo ya'duwar zina acikin al'ummah sai dai nayi babbar mantuwa. Na manta da wanu babban dalili. Wannan ba komai bane illa : Dogon Karatun Boko.

Da yawa wasu iyayen su suke jefa 'Ya'yansu akan hanyar Zina ta dalilin burinsu cewar "SAI TA GAMA DEGREE". Hakanan a bangaren Mazan ma.

Da yawa daga cikin 'Ya'ya Mata akwai wadanda tun shekarunsu basu fi sha biyar ba (15) aduniya, suke da bukatar namiji. Saboda yanayin sinadaran halittar dake jikinsu.

A bangaren Maza ma akwai da dama wadanda tun basu fi shekaru 18 zuwa 20 aduniya ba, zasu ji cewa su aure suke so!.

Kai kanka Uba idan kayi nazari da taka rayuwar zaka iya tuno cewar "TUN KANA 'DAN SHEKARA KAZA ADUNIYA KAKE DA TSANANIN BUKATAR YIN AURE".

Haka kema Uwa idan kikayi nazari zaki fahimci halin da 'Yarki take ciki. Kuma zaki iya kwatanta cewa ayanzu menene tafi bukata arayuwarta!.

Kuma ku iyaye alokacin samartakarku ko 'Yan-Matancinku babu abubuwan dake lalata zukatan yara kamar irin na wannan zamanin da muke ciki. Saboda haka yadda ke kika jure taki sha'awar, ba lallai ne 'Yarki ta iya jurewa ba. Don watakil naki iyayen sun baki tarbiyyar da ta zarce irin wacce kike yiwa taki 'Yar!.

Wasu da yawa sun san abubuwan nan da na lissafo sai dai tsananin Tsoron talauci ne yasa ba zasu amince 'Dansu yayi aure bai yi degree ba..

Suna ganin kamar "IDAN 'YARSU BATAYI DEGREE BA, BA ZATA SAMU MIJI MAI QARFIN ARZIKIN DA ZAI IYA RIKETA BA". Ko kuma idan batayi degree ta samu aikin Office ba, Ba zata samu abinda zata rike kanta agidan Miji ba..

Yarinya ta shekara 25 zuwa Talatin babu Miji babu dalilinsa wai tana karatun Boko.. Tsakani da Allah duk yadda takai wajen Lura da kanta, Ai dole Zuciyarta ta rika kawo mata wasu abubuwa. Dole wani lokacin taji ta samu matsuwar sha'awa. Kuma Kowa yasan cewa Mata sun zarce Maza wajen Matsuwa.

Sannan idan akayi La'akari da irin rayuwar da akeyi a manyan Makarantun gaba da Sakandire, za'a ga cewa ba abu ne mai Wahala ba, Yarinya ta lalace Idan har bata sanya tsoron Allah azuciyarta ba.

Ga Shaidanun Lakcharori, Ga shaidanun Samari, Ga shaidanun Qawaye.. Ga Shaidanun Whatsapp da Facebook, Ga Kuma PRESSURE na tsinanniyar sha'awa wacce Shaitan (L. A) Kullum yake chusa mata azuciya, Babu dare babu rana..

Hakanan a Bangaren Maza, Bisa irin wannan dalilan da na lissafo, Wasu sun afka cikin zina ko Luwa'di, Wasu kuma (Masu Kunya, masu Tsoron Zina) sun shiga yin Istimna'i (MASTURBATION) wanda ke mutukar chutar da lafiyarsu.

Gara namiji komai dadewa zai iya samun aure duk sanda yake so. To amma Mace fa?.

Sai ta gama bokon kuma Maza Su rika tsoron zuwa wajenta koda suna mutukar sonta da aure. Suna ganin kamar ba zata sauraresu ba.. Da haka sai ta jera shekara Uku ko hudu babu wanda yazo hira wajenta!.

Wata kuma sun rika yaudararta kenan. Wannan yazo ya yaudareta ya biya bukatarsa ya tafi, wancan ma yazo yayi ya tafi.. Ta rasa wanda zata kama balle ta tsaida Mijin aure!.

Wata kuma ta Kammale kanta. Ga ilimin ga tarbiyyar, Amma mutane su rika yi mata Mummunan zato : "Ai tunda ta dade batayi auren ban ba, to 'Yar iska ce!" (Wal Iyazu bil Lah).

Ya zama wajibi iyaye su kalli irin wadannan zantukan da idon basira, domin daukar Matakin gyarawa. Ku rika barin 'Ya'yanku suna yin aure tun auren yana sonsu!!.

Kuyi ma 'Yarku aure da zarar ta samu Manemi.. Domin Muhimmancin auren yafi na karatun boko din. Idan ma ya zama dole sai tayi, to tun farko kuyi yarjejeniya tsakaninku da Mijinta cewar zai barta ta Qarasa karatunta. Shikenan.

Hakanan 'danku Namiji : In dai har zaku iya kashe masa Makudan Kudade don yayo Degree ko Masters to mai zai hana kuyi masa auren Ku dauki nauyin rike masa Matar tasa, yaje yayi karatun? Ko kuma ku turasu su tafi tare?.

'Ya'yanku Amanar Allah ce ahannunku. Kuma sai ya tambayeku game dasu. Don haka Ku kiyaye musu :

TARBIYYARSU. 
IMANINSU. 
MUTUNCINSU.

Ku kuma 'Yan uwa 'Yan Boko kuji tsoron Allah ku kiyaye kanku daga afkawa cikin wannan mummunar bala'i wacce ta mamaye Matasa awannan zamani. Ku sani cewa jikinku Amanar Allah ne da ya baku. Kuma akwai ranar da zaku tsaya agabansa, Kowacce ga'ba tayi bayanin abubuwan da kuka aikata da ita.

Ire-iren wadannan batutuwan sune abinda ya kamata Malamai sufi mayar da hankali akai (Wato Gyaran Zukatan Al'ummah da kuma 'dinke 'barakoki acikin al'ummah) ba wai zagi ko gaba ko cin mutuncin juna ba.

Allah yasa mu gyara, Allah shi taimaki Musulunci da Musulmai. Allah shi kiyaye mana yaranmu da Qannenmu da Matanmu da zuriyarmu da dukkan Musulmai baki daya daga sharrin Zina da dangoginta. Ameeeen.

HANYOYIN RABUWA DA MASTURBATION

Hakika matsalar Istimna'i (wato Masturbation) gagarumar matsala ce wacce take shiga zuciyar masu yinta, tayi KAKA-GIDA. Kuma tana da wahalar fita gaba dayanta dole sai dai albarkacin addu'a da kuma yawaita ibada mutum zai samu wadatuwar tsoron Allah azuciyarsa harma ya zamto ba zai iya aikatawa ba.

Mafiya yawan samari suna yi ne bisa niyyar wai zasu kauce ma ZINA. Basu san cewa shima wannan din babban Kaba'ira bane!!

Matasa Maza da Mata da dama sun afka cikin wannan bala'in. Wasu cikin rashin sanin illolinsa, wasu kuma saboda tsabar Fajirci.

Kuma kamar yadda zina take da mutukar Illa tana cutar da lafiyar mutum, ta chutar da hankalinsa, da gurbata tunaninsa, ta cire masa Kwayar Imani da tsoron Allah daga zuciyarsa, to hakanan shima Istimna'i yake lalata rayuwar mutum da mutuncinsa da lafiyarsa.

Lallai wajibi ne ga duk mutumin da yake son kansa da arziki, kuma yake fatan gamuwa da Allah lafiya, ya nisanci Zina da dangoginta irin su Luwadi, Madigo, Istimna'i, da sauransu.

Kamar yadda muka sha fada anan ZAUREN FIQHU, Babbar hanyar da zaka bi/zaki bi domin rabuwa da wannan bala'in sun hada da:

1. Nisantar duk wani hoto ko Video mai nuna tsaraici. (Ka gogeshi daga wayarka)

2. Nisantar shafukan Internet masu nuna tsaraici.

3. Dena abota da fitsararrun abokai / Qawaye.

4. Nisantar duk wajen da ake chudanya tsakanin maza da mata.

5. Ka dena zama kai kadai acikin daki in dai ba ibada kake yi ba.

6. Yawaita karatun Alqur'ani da zikirin Allah. da sauran ayyukan alkhairi.

7. Zama cikin Mutanen kirki, karanta labaran mutanen kirki tare da kokarin koyi dasu.

8. Tuna Allah ako yaushe da kuma tunowa kusancinsa gareka aduk inda kake.

9. Tuna kusancin ajalinka, fitar ruhinka, kwanciyar Qabarinka, Awun hisabinka, da kuma masaukinka na karshe. Wuta ko Aljannah.

10. Fita daga duk wani Group ko shafi na batsa a Facebook ko Whatsapp wanda suke Qunshe da abubuwan batsa, tare da nisantar Friends masu sharing din irin wannan.

Illolin zina da luwadi da madigo (1)...

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin Manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam) tare da alayensa da sahabbansa. Bayan haka, wannan tsokaci ne a kan ma’ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncin kowanensu a karkashin shari’ar Musulunci da Dokta Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo ya rubuto kuma muka ga ya dace a sanya a wannan fili don amfanin jama’a. Ina rokon Allah Ya sa abin ya yi tasiri a kan kowane Musulmi. Bismillah! 
Ma’anar zina da hukuncinta:
Lafazin zina a shari’ance yana nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure, ko an mallake ta a matsayin baiwa ba. Sai dai akan yi amfani da lafazin zina a kan abin da bai kai saduwa ba, kamar yadda ya zo a Hadisin Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ) ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “An rubuta wa dan Adam rabonsa na zina, babu makawa sai ya same shi, zinar idanu ita ce gani, zinar kunnuwa ita ce ji, zinar harshe ita ce magana, zinar hannu ita ce damka, zinar kafa ita ce taku, zuciya kuwa tana kwadayi tana fata, farji kuma shi yake gaskata haka ko ya karyata.” Muslim.
A cikin wannan Hadisi za mu ga yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nuna cewa kowane dan Adam an rubuta masa rabonsa na zina, kuma zai samu wannan rabo babu makawa, sai dai ba za a kama shi da laifi ba, har sai idan ya gaskata abin da idonsa ko kunnensa ko hannunsa ko kafarsa suka jiyar da shi, ta hanyar yin amfani da farjinsa don biyan bukatar wadannan gabbai. Wannan shi ne ma’anar fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a karshen Hadisin, “farji shi yake gaskata haka ko ya karyata.” (Sharhin Sahih Muslim na Imam Nawawi Juz’i na 16, shafi na 216).
Hukuncin zina: 
Zina haramun ce a addinin Musulunci. Allah Madaukakin Sarki Ya haramta ta inda Yake cewa : “Kada ku kusanci zina, domin ita alfasha ce kuma tafarki ne mummuna.” (Isra’i:32).
Malamai suna cewa, fadin Allah “kada ku kusanci zina,” kai matuka ne wajen hana ta, don ya fi a ce “kada ku yi zina.”
Sheikh Abdur-Rahman Assa’idiy yana cewa: “Hani ga a kusanci zina ya fi kai matuka a kan hana yin ta, saboda cewa kada a kusance ta ya hada hana dukkan yin abubuwan da suke gabatar ta kuma suke kawo yin ta, domin kuwa duk wanda ya yi kiwo a gefen shinge, to ko yana daf da fadawa cikinsa, musamman ma a kan irin wannan lamari, wanda da yawa daga cikin zukata suna dauke da abin da yake sawa a afka masa. Sannan Allah Ya siffata zina da cewa alfasha ce. Ma’ana zina wata aba ce da shari’a da hankali suke ganin muninta, saboda keta alfarmar Ubangiji ce da shiga hakkin macen da hakkin danginta da mi
2018-06-22 01:19 · Reply · (0)
Sulaiman Muhammad * ibnhujjah Assalamualaikum warahatullah wabarkatahu,
Tambayana anan shine, malam minene isnadi na wannan hadisin
KU KIYAYI ZINA

A’amash ya ruwaito daga Sufyan daga Huzaifah bn Alyaman (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:

“YA KU JAMA’AR MUSULMAI, INA GARGADINKU AKAN ZINA (KU NISANCETA). DOMIN ACIKINTA AKWAI ABUBUWA GUDA SHIDA :

GUDA UKU ADUNIYA, GIDA UKU KUMA A LAHIRA. AMMA WADANDA SUKE ANAN DUNIYA SUNE :

1. Gushewar Kwarjini.

2. Dawwamammen Talauci.

3. Gajartar rayuwa (Wato rayuwarsu ba zatayi tsawo ba).
AMMA WADANDA ZASU RISKA A LAHIRA SUNE :

1. Fushin Allah.

2. Mummunan Hisabi.

3. Dawwama acikin Wuta.

A duba littafi mai suna “Akhbarun Nisa’, babin dake magana akan haramcin zina.

Shin dama mazinaci idan ya mutu yana zina, ashe zai dawwama acikin wuta,?kamar yadda wannan hadisin yayi bayani.

Wassalmu alaikum warahatullah wabarkatahu.
2021-09-15 22:15 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

PAGES ZONE

TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA

Rubuta Word:

Online : 1 user
Today : 21 user
This Week : 44 user
This Month : 67 user
Total all : 270250 visitorsUnited States
LAST PAGES