Teya Salat

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

*Post reply · Invite friends · From end
* ibnhujjah Via Dr. Aliyu Muh'd Sani

NAZARI A KAN HUJJOJIN DR. GUMI NA KORE SHIGAN ALJANI JIKIN MUTUM

Babban dalilin Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi a kan fahimtarsa ta kore shigan Aljani jikin Dan-Adam shi ne fadin Allah Madaukaki:
{ إِنَّهُ لَيْسَ لَهُ سُلْطَانٌ عَلَى الَّذِينَ آمَنُوا وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ (99) إِنَّمَا سُلْطَانُهُ عَلَى الَّذِينَ يَتَوَلَّوْنَهُ وَالَّذِينَ هُمْ بِهِ مُشْرِكُونَ (100)} [النحل: 99 - 100]

Inda Dr. yake ganin cewa; Shaidan ba zai shiga jikin Dan-Adam ba, saboda Allah ya ce:
{ إِنَّهُ لَيْسَ لَهُ سُلْطَانٌ... }

{Lallai shi ba shi da wani Sultani…}

Dr. yana fassara "Sultani" da ma'anar "karfi da iko", kamar yadda yake a Lugah. Ibnu Faris ya ce:
(سلط) السين واللام والطاء أصل واحد، وهو القوة والقهر.
مقاييس اللغة (3/ 95)

To sai dai wannar Aya ba "Nassi Sarihi" ba ne a kan ma'anar, saboda "Sultan" yana zuwa da ma'anar "Hujja" a Lugan.
Al- Jauhariy ya ce:
والسلطان أيضا: الحجة والبرهان
الصحاح تاج اللغة وصحاح العربية (3/ 1133)

Shi ma Ibnu Faris da ya cigaba da magana sai ya ce:
والسلطان: الحجة.
مقاييس اللغة (3/ 95)

Saboda haka ashe Kalmar "Sultan" bisa ma'anar "karfi da iko" ba za ta zama Nassi Sarihi ba, saboda tana daukar ma'ana fiye da daya.

Da wannan muke jayayya wa Dr. Gumi a kan ma'anar Ayar, muke cewa: Ayar ba Nassi Sarihi ba ce kamar yadda shi yake dauka.

Abin Tambaya: Mecece ma'ana mafi rinjaye ta kalmar "Sultan" a cikin Ayar daga ma'anonin guda biyu?

Lallai ma'anar "Sultan" a cikin Ayar ita ce: "Hujja". Saboda dalilai kamar haka:
1- Abdurrazzaq, Ibnu Jarir da Ibnu Abi Hatim duka sun ruwaito:
عن ابن عباس، قال: «كل سلطان في القرآن فهو حجة»
تفسير عبد الرزاق (2/ 328) تفسير الطبري ت شاكر (19/ 444) ، تفسير ابن أبي حاتم - محققا (3/ 1030)
Bukhari ma ya ambace shi a rataye babu Isnadi.
صحيح البخاري (6/ 83).

Sai Ibnu Hajar ya ce:
وصله بن عيينة في تفسيره عن عمرو بن دينار عن عكرمة عن بن عباس وهذا على شرط الصحيح
فتح الباري لابن حجر (8/ 391)

Ma'ana; Ibnu Abbas (ra) ya ce: "Dukkan kalmar "Sultan" a cikin Qur'ani ma'anarta ita ce Hujja".

2- Kuma har a Lugah ma haka abin yake, an fi rinjayar da wannar ma'anar:
Al- Zajjaj ya ce:
والسلطان في اللغة الحجة، وإنما قيل للخليفة والأمير سلطان لأن معناه أنه ذو الحجة.
معاني القرآن وإعرابه للزجاج (2/ 123)

Haka Al- Azhariy ya hakaito daga Farra'u ya ce:
قال الفراء: السلطان عند العرب: الحجة، ويذكر ويؤنث، فمن ذكر السلطان ذهب به إلى معنى الرجل، ومن أنثه ذهب به إلى معنى الحجة.
تهذيب اللغة (12/ 235)

3- Jumhurin Malaman Tafsiri suna fassara "Sultan" a cikin Ayar ne da ma'anar "Hujja".
Ibnu Jarir ya ce:
فإنه يعني بذلك: أن الشيطان ليست له حجة على الذين آمنوا بالله ورسوله...
تفسير الطبري ت شاكر (17/ 294)

"Yana nufi da Ayar cewa; Lallai Shaidan ba shi da HUJJA a kan wadanda suka yi imani da Allah da Manzonsa…".
Kuma ya ruwaito hakan daga Mujahid.

Al- Wahidiy ya ce:
قوله: {إنه ليس له سلطان على الذين آمنوا} [النحل: 99] يعني به سلطان الإغواء، وهو معنى قول المفسرين: ليس له حجة.
التفسير الوسيط للواحدي (3/ 84)

"Yana nufin ba shi da "Sultan" na batarwa, shi ne ma'anar fadin Malaman Tafsiri: ba shi da HUJJA a kan hakan.

Al- Shaukaniy ya ce: Al- Wahidiy ya hakaito Ijma'in Malaman Tafsiri a kan fassara "Sultan" a cikin Ayar da "Hujja".
وحكى الواحدي عن جميع المفسرين أنهم فسروا السلطان بالحجة.
فتح القدير للشوكاني (3/ 231)

Da wannan ya bayyana mana cewa; Ayar ba Nassi Sarihi ba ce wajen kore shigan Aljani jikin Dan-Adam.

Sai dalili na biyu da Dr. yake ambata, wato Hadisin Ibnu Abbas (ra) kamar haka:
عن ابن عباس قال: جاء رجل إلى النبي -صلى الله عليه وسلم-، فقال: يا رسول الله، إن أحدنا يجد في نفسه، يعرض بالشيء، لأن يكون حممة أحب إليه من أن يتكلم به، فقال: "الله أكبر، الله أكبر" الحمد لله الذي رد كيده إلى الوسوسة" قال ابن قدامة: "رد أمره" مكان: رد كيده".
سنن أبي داود ت الأرنؤوط (7/ 435)، مسند أحمد ط الرسالة (4/ 10)، صحيح ابن حبان - مخرجا (14/ 67)

To wannan Hadisi bai kore shigan Aljani jikin mutum ba, iyakacin abin da yake nunawa shi ne; mafi karancin kaidin Shaidan ga mutum shi ne ya sanya masa wasiwasi, kamar yadda kuma yana da wasu hanyoyin kaidin da suka fi wasiwasin girma.

In kuma Dr. yana ganin lallai Hadisin ya kore shigan Aljani jikin Dan-Adam, to sai mu ce masa; ai akwai Hadisi da ya fi wannan karfi, wanda ya tabbatar da shigan Shaidan jikin Dan-Adam, wato Hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito daga Safiyya Matar Annabi (ra), da kuma Muslim daga Anas bn Malik (ra):
«إن الشيطان يجري من ابن آدم مجرى الدم»

"Lallai Shaidan yana gudana a cikin magudanan jinin Dan-Adam".

Wannan Nassi ne Sarihi a kan shigan Aljani jikin Dan-Adam, wancan kuma ba Nassi ba ne kamar yadda yake a fili. In kuma akwai karo a tsakaninsu to wannan ya fi wancan karfi da inganci.

In kuma Dr. ya yi da'awar cewa; wannan Hadisi na gudanar Shaidan a cikin jikin Mutum ya saba waccar Aya da ta gabata, saboda a wajensa ma'anar "Sultan" a cikin Ayar ita ce: Karfi da Iko, to sai mu ce masa:
1. Wannar Fassara ba ita ce mafi rinjaye ba, a bisa fassara mafi rinjaye Hadisin bai yi karo da Ayar ba. Saboda ma'anar "Sultan" a cikin Ayar ita ce: Hujja, ba karfi da iko ba.
2. Ko da za mu sallama masa a kan fassarar tasa, ya ce: Hadisin ya saba ma Ayar don haka ba za a yi aiki da shi ba, a bisa Qa'idar wasu Malaman Usulu ta ajiye Hadisi Ahaad in ya saba ma Umumin Qur'ani, to sai mu ce:

Wannan Hadisin zai khassase Ayar, sai ace; Shaidan ba shi da ikon batar da wadanda suka yi imani, duk da cewa; yana shiga jikin Mutum ya gudana a magudan jininsa.

Don haka Hadisin ya ware gamayyar Ayar, kamar yadda hakan shi ne magana mafi rinjaye a wajen Jumhurin Malaman Fiqhu.
Al- Qarafiy ya ce:
ويجوز عندنا وعند الشافعي وأبي حنيفة تخصيص الكتاب بخبر الواحد...
شرح تنقيح الفصول (ص: 208)

"A wajenmu (mu Malikiyya) da kuma Shafi'iy da Abu Hanifa ya halasta a khassase Qur'ani da Hadisi Ahaad…".

Kuma Dalalar Hadisin shi ya fi karfi a kan Dalalar gamayyar Ayar, shi ya sa Qarafiy din ya ce:
أما دلالة العموم وتناوله الصورة التي تناولها خبر الواحد فأضعف من دلالة خبر الواحد عليها
شرح تنقيح الفصول (ص: 209)

3. In kuma Dr. yana daukan Hadisin a matsayin daga Bola aka dauko shi, to ai Hadisin Bukhari da Muslim ya fi karfi a kan Hadisin Ibnu Abbas (ra) da shi yake kafa hujja da shi, wanda Ahmad, Abu Dawuda da Ibnu Hibban suka ruwaito. In haka ne to shi ma ya dauko Hadisi daga Bola ya kafa hujja da shi kenan, tun da a bisa ka'idarsa, wannan ma Hadisin Bola ne.

A takaice, kwata – kwata babu hujja ga Dr. Gumi a cikin Aya da Hadisin da yake kafa hujja da su a kan kore shigan Aljani jikin Dan-Adam. Don haka muna fatan Dr. zai kara yin nazari a kan ma'anoninsu.
2018-06-19 16:52 (edited 2018-06-19 16:58 by ibnhujjah ) · Reply · (0)
sulaiman abdulmalik * ibnhujjah Slm, toh yansu karatun musullunci yakare sai maganan aljanun a jinkin mutun ne. in a nigeria kuke dan Allah ku shiga kawyuka kuga irin bidia da ake tabkawa.Babu dawa ko kobo. Inna muka bar maganan shirka, sallah, azumi, zakkah da uwa uba siyasa da take su ta chinnye mu a nigeria. Dobi batta lokacin wannan rubuttu bayan dawwa dagacikin alumma baiyya sarki ba, alwala,sannan sallah. Dan Allah ayi dawa ta gaske ba sukkan malanmin danuwwan ka ba a online, samme shi a gida kuyita.wannan nunine na rabuwan kai.
2018-09-25 08:55 · Reply · (0)

Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 12 user
This Week : 12 user
This Month : 100 user
Total all : 270366 visitors
LAST PAGES