ibnhujjah
*YA SAKE MU SAKI DAYA, SAI YA MUTU KAFIN MU GAMA IDDA, KO MUNA DA GADONSA?*
*Tambaya:*
Malam mutum ne yana cikin halin rashin lafiya, ya saki matansa har guda biyu saki daya, kuma bai dawo da su ba har ya mutu, kuma ba su gama iddah ba, yaya za'a yi ? za su yi masa takaba, kuma suna da gadonsa, ko ko a'a ?
*Amsa:*
To dan'uwa mutukar yadda ka sifanta, haka abin yake, to za su bar iddar saki, su koma iddar mutuwa, kuma za su ci gadonsa, saboda suna nan a matansa, tun da saki daya ne, Ibnu-khudamah ya hakaito ijma'in malamai akan haka.
Don neman Karin bayani duba : Al-mugni 8.
Allah ne mafi sani .
915
Amsawa: Dr Jamilu zarewa.