Snack's 1967

Contact Us
ISLAMICFORUM.Com.Ng™

* ibnhujjah in Allah: ((Ku yi magani lalle Allah Mabuwayi bai sanya wata cuta ba face sai da ya sanya mata magani, in banda cuta guda’ watau tsufa)). Abu Dawud, da Tirmizi, da Ahmad ne suka fidda shi.
Ana daukan allurar rigakafin cutar polio a matsayin jinya na kariya daga cutar da ake tsoron aukuwarta kafin ta auku, abin da ake kira da harshen zamani magani irin na kariya, hakika Musulunci ya tabbatar da wannan matsayi, saboda ya zo daga Annabi mai tsira da amincin Allah cewa: ((Wanda ya karya da dabino bakwai daga cikin dabinon Madina, to sihiri ko guba ba zai cutar da shi ba)). Buhari ne ya ruwaito shi. Kamar yadda ya tabbatar da shi har yanzu a cikin ka’idodin da ake bi domin a hana yaduwar cuta mai yaduwa cikin jama’a, an karbo daga Annabi mai tsira da amincin Allah cewa ya ce: ((Idan kun ji labarin aukuwar annoba a wata kasa, to kada ku shige ta, idan kuma annoba ta auku a kasar da kuke cikinta to kada ku fita daga cikinta)). Buhari ne ya ruwaito shi.
Musulunci yana kira zuwa ga fa’idanta daga dukkan wani bincike, ko wani ci gaba da aka samu na ilmin kimiyya wanda zai saukake rayuwar mutum a wannan Duniya… Lalle shi ya zo ne domin ya tabbatar da alherin mutane da jin dadinsu Duniya da Lahira, Madaukaki Ya ce: ((Ku tambayi ma’abuta ambato in har ku ba ku sani ba)). Annahl: 43. Mai tsarki Ya ce: ((Ba mu aiko ka ba face a matsayin rahama ga Duniya)). Al-Ambiya: 107.
Lalle tunkude cutuka ta hanyar yin allurar rigakafi ba ya karo da yin tawakkali, kamar yadda tunkude yunwa, da kishin ruwa, da zafi, da sanyi, ta hanyar yin kishiyoyinsu ba ya karo da shi tawakkalin, a gaskiya ma hakikanin tawakkali ba ya cika sai an yi riko da sabuba na fili wadanda Allah Madaukaki Ya kafa su domin su rika samar da abin da suke sabbabawa ne bisa kaddara da Shari’ah, saboda haka yana yiwuwa barin yin allurar rigakafi ya zama haram matukar dai hakan zai cutar. Wannan shi ne abin da aka rubuta a takaice.
Allah Ya yi dadin tsira da aminci ga shugabanmu Muhammad da iyalansa da sahabbansa da wadanda suka bi shi da kyautayi har zuwa ranar Kiyama.
Sakataren Babbar Majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya
Professor Ahmad Khalid Babakr
Cikin garin Jidda
7/6/1434
17/4/2013)). Intaha.
*************************************
Yan’uwa Musulmi wannan ita ce tarjamar fatawar Babbar Majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya game da allurar rigakafin cutar polio, manufarmu da kawo wannan fatawar shi ne fa’idantar ‘yan’uwa Musulmi na wannan kasa tamu Nigeria, saboda su san mene matsayin majoratin Maluman Musulunci na Duniya game da wannan allura ta rigakafin cutar polio.
Sannan ina jan hankalin ‘yan’uwa da su rika yin taka tsantsan cikin lamuransu, su daina gina lamura a kan aatifah ko son wani kawai, ko kuma kin wani kawai, waji bi ne a rika hankalta game da yadda lamura ke kasancewa har su cutar da mutane, ko kuma yadda suke kasancewa har su amfanar da mutane.
Lalle zai zama abin mamaki matuka mutane su ki karban shaidar mafiya yawan likitocin Duniya, sannan kuma su karbi shidar mainoratinsu wacce ta saba wa shaidar mafiya yawan!!
Haka nan zai zama abin mamaki matuka mutane su yi watsi da fatawar Majoratin Maluman Musulunci na Duniya, su koma suna yi musu jamhuri da yarfe suna cewa su ‘yan kanzagin Yahudawa ne, su mutane ne da kafurai suka ba su kudi domin su cutar da al’ummar Musulmi, sannan kuma wai suna yin dukkan abin nan da suke yi ne saboda dogara da wata fatawa da wasu mainorati suka bayar.
Haka nan abin mamaki ne matuka, mutane su karyata gwamnatocin kasashe wadanda babban aikinsu shi ne lura da maslahar jama’arsu cikin fannoni daban daban cikinsu kuwa har da fannin kiwon lafiya, su karyata gwamnatocin su daura yin yaki da su ko dai da baki ko kuwa da alkalami, wasu ma har da makami domin akwai masu kai wa masu aikin allurar rigakafin cutar polio hari da makami su kuma kashe wadanda kwanansu suka kare, saboda kawai dogara da bayanan da wasu daidaiku cikin al’umma suka fada!!!
Lalle irin wannan manhaji gairi mahsuubil awaaqib shi ne yake kawo hargitsi cikin Kasa da Al’ummah, kuma su jahilai har kullum irin wannan yanayi suke so, inda nan da nan sai ku ga cewa sun fara fiskantar mutane da fasikantarwa, sai kuma kafirtawa, daga nana sai kuma kawo musu hari bisa hujjar cewa su makiya al’ummar Musulmi ne wadanda suka karbi kudin Yahudawa domin cutar da Al’ummah!!!
Lalle mu a wannan Kasa ya kamata mu fi kowa takatsantsan, saboda har yanzu ba mu fita ba tukun daga musibar wadanda suka haramta karatun boko, saboda kawai su a ganinsu karatun boko yana karo da addinin Musulunci yana kuma cutar da Musulmi cikin addininsu, suna da irin shubuhohi nasu da suke ambatawa, amma dai majoratin maluman Musulunci sun san da cewa su ‘yan hayaniya ne kawai, kuma wannan lamari nasu babu abin da yake yi face cutar da Musulunci da Musulmi.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya ba mu ikon aiki da ita ya nuna mana karya karya ce ya ba mu ikon guje mata. Ya kuma raba wannan Al’ummah da sharrin ‘yan hayaniya da jahilai cikin rigar malamai. Ameen.
DR IBRAHIM JALO JALINGO
2018-02-23 17:34 · Reply · (0)


Online: Guests: 1




PAGES ZONE



TOP SITES
Click islamicpage.ga Shiga Forum Dinmu Na Musulunci, Wanda Zai Bawa Duk Wanda Yayi Regista A Cikinsa, Damar Postings Da Sauransu. islamicpage.ga
Click HERE Shiga Karuttukan Maluman Sunnah A, darulfikr.com
Click HERE Shiga Shafinmu Kayi Download Vedios Youtube!
Click HERE Idan Kana Sha'awar Kowan Turanci Shiga Nan !
Click Islamicfile.cf Shiga Shafinmu Na, Download Da Upload Na Musulunci, Wanda Zaka Samu Files Masu Yawa Kuma Masu Anfani And E.T.C!
Click HERE Shiga Ka Hada Logo Mai Kyau Anan Free,!
TRANSLATE
RUBUTA RA'AYINKA


Rubuta Word:





Online : 1 user
Today : 69 user
This Week : 69 user
This Month : 1022 user
Total all : 271288 visitors
LAST PAGES